"A Soke Wannan Zaben Ayi Sabon Lale" Kwamitin Kamfen Atiku Ya Yi Kira Ga INEC

"A Soke Wannan Zaben Ayi Sabon Lale" Kwamitin Kamfen Atiku Ya Yi Kira Ga INEC

  • Kwamitin kamfen Alhaji Atiku Abubakar da Gwamna Ifeanyi Okowa sun ce ayi sabon lale kawai
  • Hakan ya biyo bayan kiran da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, yayi a ranar Litinin
  • Jam'iyyar PDP da wakilanta sun kauracewa cibiyar tattara kuri'un jiha dake birnin tarayya Abuja

Abuja - Kwamitin kamfen yakin neman shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta Peoples Demoncratic Party, PDP ya yi kira ga hukumar shirya zabe ta kasa mai zaman kanta ta soke dukkan sakamakon da aka sanar kawo yanzu.

Mai magana da yawun kamfen, Daniel Bwala ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Talata, rahoton ChannelsTV.

Bwala ya bayyana cewa:

"A dakatar da tattara zaben yanzu kuma a bada amsa game da korafe-korafen da jam'iyyu sukayi game da kin amfani da na'urar BVAS da sauya sakamako a yanar gizo."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Duk Wanda Bai Gamsu Da Sakamako Ba Ya Tafi Kotu", Martanin INEC Ga PDP Da LP

"A zabi sabon ranar gudanar da zabe a wadannan wurare kuma a tabattar da cewa an saura sakamakon. Wajibi ne a yi amfani da BVAS kan a ce zaben na gaskiya ne."
Atiku
Atiku Da Okowa Ya Yi Kira Ga INEC
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ayi watsi da dukkan sakamakon da aka sanar har zuwa lokacin da aka daura dukkan sakamako daga runfunan zabe zuwa yanar gizon INEC, kuma a sanar da su, kuma a baiwa wakilun jam'iyyu nasu kwafin."

Zaben 2023: Obasanjo Yana Kira A Yi Wa Dimokradiyya Juyin Mulki Ne, Kwamitin Kamfen Din APC Ta Yi Martani

Kwamitin yakin neman zabe dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ta ragargaji tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan kira da ya yi na cewa a soke wasu zabuka a kuma sake yinsu kan zargin magudi

Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Dele Alake, cikin sanarwar da ya fitar ya ce Obasanjo ba shi da hujja kawai ya yi wannan maganan ne kan jita-jita da ya ke ji kuma yana son yi wa dimokradiyya juyin mulki

Kara karanta wannan

2023: "Rayuwa Ta Na Cikin Hatsari", Baturen Zabe Na Jihar Rivers Ya Dakatar Da Tattara Sakamakon Zabe

Alake ya kuma ce dama Obasanjo ya riga ya zabi bangare a wannan zaben duba da cewa ya fito fili ya fada wa matasa cewa su zabi Mr Peter Obi na jam'iyyar Labour kuma ya tunatar da al'umma cewa Obasanjo ya yi zabe da ake ganin shine mafi muni a 2003 da 2007

Asali: Legit.ng

Online view pixel