Hukumar Zabe ta INEC Ta Ba Tinubu da Shettima Takaddun Shaidan Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023
- Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta mika takardun shaidan lashe zaben shugaban kasa ga Bola Ahmad Tinubu da Kashim Shettima na jam'iyyar APC
- An tashi da rahotannin cewa, Bola Ahmad Tinubu ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a Najeriya a ranar 25 ga watan Faburairun 2023
- Ya zuwa yanzu, jiga-jigan siyasa a Najeriya na ci gaba da mika sakon murna ga zababben shugaban kasan Najeriya Tinubu
FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta mikawa Bola Ahmad Tinubu, zababban shugaban kasa a Najeriya da mataimakinsa, Kashim Shettima takardun shaidar lashe zaben ranar 25 ga watan Faburairu.
Shugaban INEC, Mahmud Yakubu ne ya gabatarwa jiga-jigan siyasan biyu takardun a ranar Laraba 1 ga watan Maris da yamma a cibiyar manyan taruka ta kasa da ke Abuja, Punch ta ruwaito.
Ba da takardun na zuwa ne jim kadan bayan da hukumar ta bayyana a gidajen talabijin na Najeriya cewa, Tinubu ya fi kowa yawan kuri'u a zaben na bana.
Kuri'un da 'yan takara suka samu a zaben bana
Tinubu ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a Najeriya, inda ya samu kuri'u 8,794,726 a karkashin inuwar jam'iyyar APC.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Atiku Abubakar na PDP ne ya zo na biyu a zaben, inda ya tattara yawan kuri'un da suka kai 6,984, 520 a zaben,
A bangare guda, Peter Obi ya zo na uku, inda ya samu kuri'u 6,101,533 a karkashin inuwar jam'iyyar Labour.
Sauran jam'iyyun siyasa sun samu rabonsu daga sauran kuri'un da aka kada a jihohin kasar baki daya a ranar Asabar da ga tabata.
A tun farko, hukumar zabe ta INEC ta ce za ta ba Tinubu da Shettima takardun ne a yau Laraba 1 ga watan Maris din 2023, kamar yadda RipplesNigeria ta ruwaito.
Buni ya taya Tinubu murnar lashe zabe
A wani labarin kuma, kun ji yadda gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya taya Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa.
A cewar Buni, Tinubu ne wanda ya fi cancanta ya gaji Buhari, kuma hakan ya tabbata ta hanyar yin zaben bana.
Ya yabawa 'yan Najeriya bisa jajircewa da amincewa da jam'iyyar a cikin irin wannan yanayi mai bukatar ujila.
Asali: Legit.ng