Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Sheikh Bala Lau Ya Gargadi Yan Siyasa Kan Furta Maganganu Da Ka Iya Tada Rikici

Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Sheikh Bala Lau Ya Gargadi Yan Siyasa Kan Furta Maganganu Da Ka Iya Tada Rikici

  • Sheikh Bala Lau, shugaban kungiyar Izala a Najeriya ya ja kunnen yan siyasa su guji furta maganganu da ka iya janyo tabarbarewar tsaron kasa
  • Babban malamin na addinin musulunci ya yi wannan gargadin ne cikin wata sanarwar manema labarai a ranar Talata, 23 ga watan Fabrairu, yayin da INEC ke cigaba da tattara sakamakon zabe
  • Lau ya yi kira ga duk wani dan siyasa da ke ganin an masa ba daidai ba, ya bi tsarin da doka ta tanada don bin hakkinsa na dimokradiyya amma a guji furta maganganu da ka iya raba kan kasa

Shugaban Kungiyar Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Bala Lau ya gargadi yan siyasa a dukkan sassan kasar kan furta maganganu masu hatsari don 'kada su kawo cikas ga aikin zabe da Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa, INEC, ke yi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Duk Wanda Bai Gamsu Da Sakamako Ba Ya Tafi Kotu", Martanin INEC Ga PDP Da LP

Legit.ng ta rahoto cewa wata sanarwar manema labarai da aka fitar a ranar Talata, 28 ga watan Fabrairu, kuma dauke da sa hannun Sheikh Bala Lau a madadin kungiyar, ta ce duk wani wanda ya ke ganin ba a yi masa adalci ba ya bi tsarin doka wurin kwato hakkinsa na dimokradiyya.

Sheikh Bala Lau
Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Sheikh Bala Lau Ya Gargadi Yan Siyasa Kan Tada Rikici
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Don haka duk wanda/wacce ke ganin an danne masa hakki ba bisa ka'ida ba ya bi tsarin doka kamar yadda ya ke a cikin Dokar Zabe na kasa."
"Yana da matukar muhimmanci gare mu dukka mu sani a zuciyar mu cewa sai akwai zaman lafiya za a iya dimokradiyya. Rikici ba barazana bane kawai ga dimokradiyya amma yana iya raba kanmu a matsayin kasa," Lau ya jadada cikin sanarwar."

Babban malamin addinin musuluncin ya kuma ce:

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: A Karshe Shugaban INEC Ya Mayar Da Martani Ga Jam'iyyun Adawa

"Don haka ina amfani da wannan dama a madadin kungiyar JIBWIS Nigeria don yin kira ga dukkan yan Najeriya musamman musulmi da su nesanta kansu da tada rikici ta hanyar kiyayye furta kalamai da za su iya kawo cikas ga dimokradiiyar mu.
"Don haka dukkan mu muna da hakki da nauyi da ya rataya a wuyanmu na tabbatar da dorewat zaman tare a matsayin kasa wacce za ta cigaba da gwagwarmaya cikin zaman lafiya da lumana."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel