Ina da Ƙwarin Gwuiwa Cewar Nine Zan Lashe Zaɓen nan - Tinubu

Ina da Ƙwarin Gwuiwa Cewar Nine Zan Lashe Zaɓen nan - Tinubu

  • Tinubu Ya Dira Wajen Ne Sanya Kaya Shudi Tare da Bakar Hula Cike Da Annushuwa, Yana Dagawa Mutane Hannu
  • Bayan An Tantance Shi Kamar Yadda Tsarin Zabe Yake Ya Kada Kuri'ar sa
  • Yan Jarida Sun Masa Tambaya Bayan Zaben Inda Ya Nuna Musu Shi Ko a Jikinsa, yana Da Tabbacin Lashe Zabe

Zaɓe yana ta ƙara kankama yayin da yan takarkaru suke ta zuba luguden ƙuri'u a akwatunan su dake lungu da saƙo na ƙasar nan.

Hattana lamba ɗaya da yake jagora a jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari ya saka ƙuriar sa acan mazaɓar sa dake daura.

Ɗan takarar jam'iyyar APC na shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya saka tasa ƙuriar a can mazaɓar sa dake Ikejan Jihar Lagos.

Tinubu
Dan Takarar Jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu Yayi Kada Kuria Hoto: Facebook
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Yadda Masu Kada Kuri'a Sukayi Karanci Basu Fito ba a Kaduna Ya Dame Ni - El-Rufai.

Jim kaɗan da kada kuri'ar tasa, Tinubu ya shaidawa manema labarai cewar, tsarin mulkin demokradiyya ya samu wajen zama a ƙasar, tare da nuna ƙwarin guiwa wajen lashe zaɓen da a yanzu haka yake gudana.

Game da yadda jama'a suka amsa kira suka fito kaɗa ƙuriar su, ɗan takarar ya shaida cewar:

"Mun san za'a rina, domin tabbatuwar demokradiyya, ana buƙatar tsarin ta ya kasance mai kyau tare da maida hankali sosai wajen ganin haka ya faru." Kamar Yadda Jaridar Guardian ta ruwaito

Tinubu
Bola Ahmed Tinubu Hoto: gurdian.ng
Asali: UGC

Koda aka tambayi Tinubu ko yana ganin zai iya lashe zaɓen kuwa?

Cikin izza tare da ƙwarin guiwa ya maida martani gajere, inda yace:

"Ina da matuƙar ƙwarin gwuiwar hakan matuƙa gaya"

Idan dai za'a iya tunawa,Tinubu yana takara ne da Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na Labor Party tare da Rabi'u Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP.

Tantance masu zaɓe da ƙada ƙuria tuni aka yi nisa a mazaɓu da yawa dake lungu da saƙo na ƙasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Yayi Allah Wadai Da Kisan Ɗan Takara Ana Dab Da Zaɓe, Ya Ba Jami'an Tsaro Wani Umurni

Ana fatan ganin masu ƙada ƙuria miliyan 87.2 da suke da katin jefa kuri'a na dindindin ne zasu zaɓi shugaban ƙasa da ƴan majalisun tarayya da dattijai.

Mahukunta a hukumar INEC sun tabbatar da cewa, ana da wajen kada ƙuria kimanin 176,606 a ciki da wajen jihohi 36 da Abujan Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel