An Tafka Asarar Dukiyoyin Miliyoyin Naira Sakamakon Gobara A Kasuwar Yan Katako Na Anambra

An Tafka Asarar Dukiyoyin Miliyoyin Naira Sakamakon Gobara A Kasuwar Yan Katako Na Anambra

  • Mummunan gobara ta yi barna a kasuwar yan katako na Umoukpa da ke jihar Anambra inda ta kone a kalla shaguna guda 17
  • Cif Martin Agbili, shugaban hukumar kashe gobara na jihar Anambra ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa ba a san sanadi ba
  • Agbili ya ce jami'an hukumarsa sun yi nasarar kashe gobarar sun kuma hana ta bazuwa wasu shagunan amma an yi asarar dukiya

Jihar Anambra - Gobara ta faru a kasuwar yan katako na Umoukpa, Awka, Jihar Anambra, inda ta lalata shaguna a kalla 17 a yankin a ranar Takata, rahoton The Punch.

Duk da cewa ba a rasa rai ba, an tattaro cewa gobarar ta tashi ne misalin karfe 10.16 na dare kuma ta cigaba da ci har sai da jami'an hukumar kashe gobara na jihar suka taho wurin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bam Ya Tashi a Sakatariyar Karamar Hukuma a Arewacin Najeriya

Anambra Fire
Jami'in kashe gobara yana bakin aiki. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Ba a iya sanin sanadin gobarar ba, amma shaidun gani da ido da wadanda abin ya shafi shagunansu sun ce gobarar ta lalata dukiyoyin miliyoyin naira.

Shugaban hukumar kashe gobara na jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin

Da ya ke tabbatar da lamarin, shugaban hukumar kashe gobara, Cif Martin Agbili, ya ce jami'ansa sun yi yaki da wutan har sai da suka ci galaba suka hana gobarar bazuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Misalin karfe 10.16 na daren ranar Talata, jami'an hukumar kashe gobara na jihar Anambra, sun samu kiran neman dauki sakamakon gobara a kasuwar katako na Umuokpu Awka.
"Nan take muka tura motar kashe gobara da jaruman masu kashe gobara zuwa wurin. Daga bisani an kashe wutan cak.
"Ba a san abin da ya janyo gobarar ba kuma ba a rasa rai ba. Kimanin shaguna 17 suka kone sosai amma an iya dakatar da gobarar daga bazuwa zuwa wasu shaguna.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Jefa Bam Ofishin Yan Sanda, Sun Hallaka Jami'ai 3

"Jami'an mu sun bar wurin misalin karfe 1.06 na dare. Har yanzu muna lokacin sanyi ne, don haka ku guji duk wani abu da zai iya tada gobara. Ku tuna cewa lokacin da kuka kira yana da alaka da lokacin amsa kiran."

Gobara ta yi barna a tsohuwar kasuwa a jihar Sokoto

A wani labarin mai kama da wannan kun ji cewa gobara ta barke a tsohuwar kasuwa da ke jihar Sokoto inda ta kona a kalla shaguna 20.

Shugaban hukumar yaki da gobara, Mr Mustapha Abubakar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN cewa gobarar ta fara ne misalin karfe 11 na daren ranar Litinin har zuwa karfe 2 na dare.

Ya kara da cewa shagunan da abin ya shafa sun hada da na siyar da tufafi da kayan kwaliya a kasuwar, ya kara da cewa jami'ansu na binciken sanadin gobarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel