Za a Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Kamar Yadda Aka Tsara, Majalisar Tsaro

Za a Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Kamar Yadda Aka Tsara, Majalisar Tsaro

  • Majalisar tsaro ta kasa ta yi umurnin gudanar da babban zaben Najeriya kamar yadda aka tsara
  • Shugabannin tsaron sun bayar da umurnin yayin zamansu na yau Laraba, 22 ga watan Fabrairu wanda Shugaba Buhari ya jagoranta
  • Za a gudanar da babban zaben shugaban kasa da na yan majalisun tarayya a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu

Abuja - Majalisar tsaro ta kasa karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sanar da cewar zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya zai gudana kamar yadda aka tsara.

A ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu ne aka shirya za a yi babban zaben Najeriya inda za a fara zaben shugaban kasa da na yan majalisun tarayya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar taron majalisar tsaro
Za a Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Kamar Yadda Aka Tsara, Majalisar Tsaro Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, da Sufeto Janar na yan sanda, Usman Alkali Baba sun yi wa manema labaran fadar shugaban kasa karin haske a kan ganawarsu, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku, Tinubu Da Wasu Yan Takara Za Su Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

A gudanar da zabe ranar Asabar kamar yadda aka tsara, shugabannin tsaro

Malami ya ce shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor, hafsoshin tsaro uku, Sufeto Janar na yan sanda da shugabannin sauran hukumomin tsaro sun yi jawabi kan shirinsu na samar da tsaro a zaben ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce a kan haka, majalisar ta ba da umurnin cewa a gudanar da zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu kamar yadda aka tsara, rahoton Thisday.

A cewarsa, taron majalisar tsaron ya biyo bayan tarukan majalisar zartarwa da na tsoffin shugabannin kasa da aka yi saboda tabbatar da shirin hukumar INEC da hukumomin tsaro don ci gaba da shirin gudanar da babban zaben kasar.

Idan za ku tuna, mun kawo cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, Farfesa Mahmoud Yakubu a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

An Yi Kus-Kus Tsakanin Shugaban INEC Da Shugaba Buhari Game Da Zaben Ranar Asabar

Buhari da Farfesa Mahmoud tun tattauna kan yadda za a gudanar da zaben ranar Asabar cikin nasara a yau Laraba, 22 ga watan Fabrairu.

Hukumar INEC ta fara rabon kayan zabe

A wani labarin kuma, mun ji cewa hukumar zabe ta kasa ta fara rarraba kayan aikin zabe a ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu duk a cikin shirye-shiryen ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel