Gwamnan APC ya yi wa Emefiele Allah-ya-isa a Dalilin Canza Takardun Kudi Daf da Zabe

Gwamnan APC ya yi wa Emefiele Allah-ya-isa a Dalilin Canza Takardun Kudi Daf da Zabe

  • Abdullahi Umar Ganduje ya nesanta APC da hannu wajen canza takardun N200, N500 da na N1000
  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce babu wanda ya yi wannan aiki illa Gwamnan bankin CBN
  • Irinsu Rabiu Musa Kwankwaso da Ibrahim Shekaru duk sun yi wa Mai girma Gwamnan martani

Kano - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya sake dura kan babban bankin CBN a sakamakon canza manyan takardun kudi da aka yi.

A wani faifen sauti, an ji Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana cewa kamar yadda aka yi fama da annobar Coronavirus, haka nan CBN ya kawo COVID-23.

Abdullahi Ganduje ya shaida cewa jam’iyyar APC ba ta goyon bayan canza kudi, ya ce an yi haka ne saboda a ki zaben Bola Tinubu da Nasiru Gawuna.

Vanguard ta ce da Mai girma Abdullahi Umar Ganduje yake kaddamar da rabon kayan abincin da za a rabawa al’umma, ya soki Godwin Emefiele.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Ya Munana, Gwamnan Arewa Ya Shirya Yafe Takararsa Saboda a Doke Atiku

A wani jawabi da aka samu daga bakin Babban sakataren yada labaran Gwamnan, Abba Anwar, Ganduje ya ce za su raba abinci ne domin rage radadi.

Rahoton ya bayyana cewa Gwamnan ya caccaki ‘yan adawa musamman jam’iyyar NNPP mai sukar matsayarta, ya ce burinta shi ne a cigaba da wahala.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan Kano
Zulum, Adamu, Ganduje, Tinubu da Shettima a Borno Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Gwamna ya yi 'Allah ya isa!'

A wani faifen da yake yawo a dandalin sada zumunta, an ji lamarin ya kai sai da Gwamnan na Kano ya yi ‘Allah ya isa’ ga Gwamnan bankin na CBN.

Gwamnan ya soki bankin CBN, ya ce an jefa Bayin Allah a cikin kunci. Ganduje ya ce shi da mutanen da suka yi asara sun yi wa Mr. Emefiele Allah ya isa.

"Da farko ban goyon baya …" - Kwankwaso

Da aka zanta da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a gidan rediyo a Katsina, ya nuna cewa da farko bai goyon bayan tsarin, amma yanzu ya sake matsaya.

Kara karanta wannan

Gwamna Ganduje Yace China Ta Kawo COVID-19, CBN Ya Kawo COVID-23

‘Dan takaran shugaban kasar ya ce gwamnonin jihohi sun boye makudan kudi ne don haka suka birkice da jin Muhammadu Buhari ya kawo sabon kudi.

A wani bidiyon, shi ma tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya maidawa Gwamna mai-ci martani a kan kalaman da ya saba fada.

'Yan sanda 18, 000 za su tsare Kano

Rahoto ya nuna cewa Rundunar 'Yan Sandan Najeriya sun shiryawa duk wanda zai nemi ya kawo matsala a wajen zaben shugaban kasa da za a gudanar.

Mamman Dauda wanda shi ne Kwamishinan ‘yan sandan reshen jihar Kano ya ce an aiko jami’ai 18, 000 domin a tabbatar an yi zabe cikin zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng