Gwamna Ganduje Yace China Ta Kawo COVID-19, CBN Ya Kawo COVID-23

Gwamna Ganduje Yace China Ta Kawo COVID-19, CBN Ya Kawo COVID-23

  • Gwamnan jihar Kano ya fara rabon kayan abinci ga al'ummar jihar ana sauran yan kwanaki zabe
  • Gwamnan ya ce wannan rabo da ake yi na rage afin wahalar rashin Naira ne da jama'a suka shiga
  • Ganduje na cikin gwamnoni goma da suka shigar da gwamnatin tarayya kotu game da lamarin sauya fasalin kudi

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rabon tallafi ga al'ummar jihar Kano domin rage radadin azabar da karancin Naira ya ganawa al'ummar jihar.

Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, a ranar Litinin ya kaddamar da rabon a gidan gwamnatin jihar, rahoton Cable.

Ya bayyana cewa jiharsa ce tafi wahala da wannan tsari na sauya fasalin Naira da bankin CBN yayi.

Gwamna Abdullahi Ganduje
Gwamna Gandujea ofishinsa, yayi magana kan lamarin yunwa Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Naira: El-Rufa'i Da Yahya Bello Sun Dira Kotun Koli Inda Za'a Yanke Hukunci Yanzu

A cewarsa:

"Bamu muka kawo wannan lamarin ba, kuma bamu yi fatan ya faru da mu ba. Babu dadi ko kadan. Mun yi rabon kayan tallafi irin wannan a lokacin COVID-19."
"Yau al'ummarmu na fuskantar COVID-23 da babban bankin CBN ya haddasa."
"Da farko mun yi tunanin karamar cuta ce, amma yanzu ta zama gagarumar cuta."
"Wannan cutar da CBN ya haddasa ta shafi dukkan bankunansu, POS, na'urorin ATM, da kuma komai dake da alaka da su."
"Ba zamu daina daura laifi kan CBN ba bisa wannan babban kuskuren tattalin arziki da ya tafka."

Ganduje ya ce dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin kawo karshen wahalan idan yayi nasara.

A cewarsa, Tinubu zai tabbatar da cewa ya kawo karshen wannan lamari.

Zan Soke Tsarin Sauya Fasalin Naira Idan Na Hau Mulki, Kwankwaso

A wani labarin kuwa, daya daga cikin yan takarar kujerar shugaban kasa kuma haifaffen dan jihar Kano ya bayyana cewa zai soke dokar da aka sanya kan tsaffin kudi idan ya samu nasara a zabe.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito, An Bayyana Gwamnan PDP Da Ya Taimaka Aka Kayar da Atiku Ranar Zabe

Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa zai baiwa kowa dama ya mayar da tsaffin kudinsa banki.

Hakazalika ya yi alkawarin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi al'ummar arewa maso yammacin Najeriya.

Hukumar gudanar da zabe ta kasa za tayi zaben shugaban kasa da yan majalisar tarayya ranar 25 ga Febriaru, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel