NRC Ta Dakatar da Sufurin Jiragen Kasa a Dukkan Sassan Najeriya

NRC Ta Dakatar da Sufurin Jiragen Kasa a Dukkan Sassan Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta dakatar da harkokin sufurin jiragen kasa a sassan Najeriya saboda zuwan zaben shugaban ƙasa
  • Hukumar NRC ce ta sanar da wannan matakin a wata sanarwa da mai magana da yawunta, Mahmood Yakub, ya fitar
  • Ta ce ta yi haka ne domin baiwa mutane musamman fasinjojin jirgin kasa damar zuwa su sauke nauyin da ya rataya a kansu

Abuja - Hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ƙasa (NRC) ta dakatar da zirga-zirgan Jirgaen a dukkan sassan Najeriya daga ranar Asabar, 25 zuwa Litinin 27 ga watan Fabrairu, 2023.

Daily Trust tace NRC ta ɗauki wannan matakin ne saboda zuwa zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya wanda za'a gudanar ranar Asabar mai zuwa.

Hukumar NRC.
NRC Ta Dakatar da Sufurin Jiragen Kasa a Dukkan Sassan Najeriya Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Mai magana da yawun hukumar NRC ta ƙasa, Mahmood Yakub, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bam Ya Tashi a Sakatariyar Karamar Hukuma a Arewacin Najeriya

Sanarwan ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Duba da zaben shugaban kasa da ke tafe a ƙasar nan, majalisar shuwagabannin NRC na sanar da ɗaukacin al'umma musamman Fasinjoji cewa ta dakatar da sufurin jiragen kasa na wucin gadi."
"Babu zirga-zirgar jiragen ƙasa daga ranar Asabar 25 zuwa Litinin 27 ga watan Fabrairu, 2023 domin baiwa mutane damar sauke nauyin dake kansu."

Bugu da ƙari sanarwan ta bayyana jiragen ƙasan da matakin ya shafa wanda ya haɗa da, Abuja – Kaduna (AKTS), Warri – Itakpe (WITS), Lagos – Ibadan (LITS), da kuma sufurin jirgin ƙasan Iddo Lagos – Ijoko.

Hukumar NRC ta tabbatarwa yan Najeriya cewa sufurin jiragen kasa zai dawo kamar yadda aka saba daga ranar 28 ga watan Fabrairu, 2023, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A ranar Asabar mai zuwa 25 ga watan Fabrairu, 2023, hukumar zabe mai zaman kanta INEC zata gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Ya Hargitse, Jam'iyya Ta Ayyana Gogon Baya ga Peter Obi a Zaben 2023

Mako biyu bayan haka INEC ta tsara gudanar da zaben gwamnoni a jihohin Najeriya tare da mambobin majalisar dokokin jiha.

Oyebanji ya sake nasara a Kotu

A wani labarin kuma Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Nasarar Oyebanji a Zaben Gwamnan Ekiti

Kwamitin alkalai uku na Kotun daukaka kara mai zana a Ado Ekiti ya kori ƙarar da dan takarar SDP ya sgigar kan zaben gwamnan jihar Ekiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel