Wani Kamfanin Kasar Sin Ya Ba Ma’aikata Kyautar Tulin Tsabar Kudi, Bidiyo Ya Girgiza Intanet

Wani Kamfanin Kasar Sin Ya Ba Ma’aikata Kyautar Tulin Tsabar Kudi, Bidiyo Ya Girgiza Intanet

  • An ga wani bidiyon ma’aikata na karbar kyautar kudi daga kamfaninsu ya yadu a kafar sada zumunta, ya jawo cece-kuce
  • An ce mutum uku da suka fi kokari a kamfanin sun samu kyautar Yuan miliyan biyar kowannensu, kwatankwacin N334.7m
  • Wannan babbar kyauta ta girgiza jama’ar kafar sada zumunta, sun kuma yi mamakin karamcin wannan kamfanin

Wani bidiyo ya yi shuhura a kafar sada zumunta na wasu ma’aikatan kamfanin Henan a kasar Sin, inda aka ba su kyautar karshen shekara na tsabar kudade a hannu.

An ba mutanen ne tulin takardun kudade tsaba a hannu, inda ma’aikatan da kansu suka shiga mamaki da ta’ajibi.

A cewar rahoton jaridar South China, mutum biyar da suka fi kokari a kamfanin sun samu kyautar Yuan miliyan biyar, kwantankwacin N334.77m kowanne daga cikin kyautar kudi Yuan mikiyan 61 (N4.08bn) da kamfanin ya yi.

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Ekiti

Yadda aka rabawa ma'aikatan kamfani a kasar Sin
Wani Kamfanin Kasar Sin Ya Ba Ma’aikata Kyautar Tulin Tsabar Kudi, Bidiyo Ya Girgiza Intanet | Hoto: @today
Asali: Facebook

An yi gasar kirga kudi, an kashe miliyoyi

AsiaOne ta ruwaito cewa, sauran ma’aikatan kuma sun halarci gasar kirga kudaden, inda aka baje musu ‘yan 100 na takardun Yuan a kan teburi su yi da kirgawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daya daga cikin masu gasar kirge ya tashi da Yuan 157,000, kuma kamfanin ya kashe akalla Yuan miliyan 12 a gasar kirga kudin.

Hakazalika, kamfanin ya yarabawa dukkan ma’aikatan Yuan 300 kowanne a matsayin kyauta haka siddan.

Al’adar kamfanonin kasar Sin ne yin irin wannan bikin

Bidiyon da aka yadan dai ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta, inda mutane da yawa ke yaba kokarin kamfanin wajen yaba kokarin ma’aikata ta hanyar ba su kyautar kudi mai tsoka.

Duk da haka, an ce wannan ba sabon abu bane a kamfanonin kasar Sin, domin akan karrama jajirtattun ma’aikata da kyauta mai tsoka.

Kara karanta wannan

Kuna cutar da talakawa: Atiku ya caccaki CBN da Buhari kan sabuwar dokar kudi

Ana ganin hakan a matsayin hanya mai jan hankalin sauran ma’aikata, kuma yakan karawa sauran na kasa kwazo da mai da hankali kan aiki.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Low Seow Chay:

"Kamfanonin Sin na kuma yin gasar kwadanda suka fi kwazo da fikira daga ma’aikatan gudanarwa. Sukan biya rmb miliyan 1 ko 2 a shekara a matsayin albashi wannan ba an saba gani.”

Robert JO:

"Wannan abu ya yi kyau...Ina ganin idan ka raba kudi saboda aiki tukura. Kana karfafa mutane su yi aiki tukuru. Hakan na da kyau.

Carmi Macayan:

"Abin al’ajabi. Yaushe manyan kamfanoninmu za su yi haka ga ma’aikatansu.

Charles Misong:

"Wannan kamfanin zai ci gaba da yin sama saboda kyautatawa ma’aikatansa.”

A nan gida Najeriya kuma, an gwarzon malamin shekara a jihar Legas kyautar N20,000, hakan ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.