'Yan Ta'adda Sun Cinna Wa Dattijuwa Wuta Da Ranta Ta Ƙone Ƙurmus
- Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai mummunan hari garin Amagu Ihube da ke karamar hukumar Okigwe na jihar Imo a ranar Talata
- Yayin harin, yan bindigan sun cinna wa gidajen manyan mutane da dama wuta a daya cikin gidajen sun halaka wata dattijuwa da ranta
- Emeka Okoronkwo, tsohon kwamishinan wasanni da matasa na daga cikin wadanda aka kona wa gidajensa a kauyen kuma ya tabbatar wa manema labarai hakan
Jihar Imo - Wasu yan ta'adda sun kona wata dattijuwa kurmus lokacin da suka cinna wa wasu gidaje wuta a ranar Talata a garin Amagu Ihube da ke karamar hukumar Okigwe da ke jihar Imo a ranar Talata.
A cikin gidajen da aka kona akwai gidan kwamishinan jihar Imo na matasa da wasanni, Emeka Okoronkwo da ke kauyensu, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuma kona gidan tsohon shugaban tsangayar koyan aikin lauya na Jami'ar Jihar Imo da ke Owerri, Nnamdi Obiaraeri, wanda ya yi aiki a matsayin kwamishinan labarai, matasa da wasanni da kuma kwamishinan filaye da tsara birni lokacin mulkin gwamna Ikedi Ohakim da Rochas Okorocha kamar yadda aka jero.
Hakazalika, an kona gidan tsohon direktan hukumar yan sandan farin kaya, DSS, Emeka Ngwu, wanda ya dade da murabus.
Daily Trust ta rahoto cewa dattijuwan tana gidan Ngwu a lokacin da wutar ta fara ci.
An kuma kona gidajen wasu fitattun mazauna garin yayin harin.
Okoronkwo ya tabbatar da harin
Yayin zantawa da manema labarai a ranar Talata, Okoronkwo ya tabbatar da harin da aka kai gidan sa.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Imo, ASP Henry Okoye shi ma ya tabbatar da harin.
Ya ce yan sanda sun kaddamar da bincike kan afkuwar lamarin, ya kara da cewa kawo yanzu ba a kama kowa dangane da zargin hannu a harin ba.
Yan ta'adda sun kashe dan sanda da wasu mutane 22 kuma sun cinna wa gidaje 50 wuta a jihar Binuwai
A wani rahoton da muka kawo a baya kun ji cewa yan bindiga sun halaka a kalla mutane 23 ciki har da jami'in dan sanda a wani mummunan hari da suka kai a Gbeji da ke karamar hukumar Ukum na jihar Binuwai.
Laftanat Paul Hembah (mai murabus), mashawarcin gwamnan jihar Binuwai kan harkokin tsaro ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa an yi wa dan sanda mummunan rauni kuma ya cika a hanyar zuwa asibiti.
Asali: Legit.ng