Ramadan Ya Matso: Sarkin Musulmi Ya Umarci A Fara Duba Jinjirin Watan Sha'aban

Ramadan Ya Matso: Sarkin Musulmi Ya Umarci A Fara Duba Jinjirin Watan Sha'aban

  • Fadar mai Alfarma Sarkin Musulmai ta bukaci a fara duban jinjirin watan Sha'aban 1444 AH daga ranar Litinin
  • A wata sanarwa da Sultan ya fitar ranar Lahadi, ya ce ranar Litinin ta kama 29 ga watan Rajab, 1444 AH daidai da 19 ga watan Fabrairu, 2023
  • Daga watan Sha'aban sai watan Ramadana wanda Musulmai ke azumtar shi baki ɗaya kamar yadda Addini ya wajabta masu

Sokoto - Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Sa'ad Abubakar III (Sultan na Sakkwato) ya fitar da sabuwar sanarwa.

Sultan ya umarci ɗaukacin al'ummar Musulmai a Najeriiya su fara duba jinjirin watan Sha'aban 1444 AH daga ranar Litinin 29 ga watan Rajab, 1444 daidai da 20 ga watan Fabrairu, 2023.

Sarkin Musulmai.
Ramadan Ya Matso: Sarkin Musulmi Ya Umarci A Fara Duba Jinjirin Watan Sha'aban Hoto: Sultan
Asali: Twitter

Sarkin Musulmin ya ba da wannan umarni ranar Lahadi a Sakkwato a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin harkokin addini na fadar Sultan Sakkwato.

Kara karanta wannan

An Gurfanar Da Abokan Murja Kunya Bisa Yada Batsa Ta Shafin TikTok

Jaridar Daily Trust ta rahoton Sanarwan na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Muna sanar da ɗaukacin al'ummar Musulmai cewa ranar Litinin 29 ga watan Rajab, 1444 AH wacce ta yi daidai da 20 ga watan Fabrairu, 2023, ita ce ranar da ya kamata a fara duba jinjirin watan Sha'aban, 1444 AH."
"Saboda haka muna buƙatar Musulmai su fara duba jinjirin watan Sha'aban daga ranar Litinin kuma su kai rahoto ga Hakimi ko Dagacin gari mafi kusa idan sun ga watan domin sanar da Sultan."

Bayan haka Sultan ya roki Allah SWT ya shiga lamarin Musulmai ya basu karfin ikon sauke hakkoki da nauyin da addini ya ɗora masu, Ameen, kamar yadda PM News ta rauwaito.

Watan Sha'aban shi ne wata na 8 a cikin jerin watannin Kalandar Musulunci kuma shi ne watan da Ramadan ke biye masa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Emefiele Ya Dira Fadar Shugaban Kasa, Ya Bukaci A Bi Umurnin Buhari Kan Sauyin Naira

A watan Ramadan ne Allah ya shar'anta wa Musulmi Azumi tun daga farko har ƙarshe kuma watan na da dumbin falala sannan daren Lailatun kadari na zuwa a cikin watan na Azumi.

Sauya Naira: Mutane Suna Cikin Yunwa Kuma Sun Fusata, Sultan

A wani labarin kuma Sarkin Musulmai a Najeriya ya yi magana kan halin da ake ciki sakamakon sauya fasalin naira da CBN ya yi

Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ce mutane sun shiga halin ƙunci da kuma yunwa kuma basu samun sabbin kuɗin domin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.

Basaraken ya faɗa wa gwamnati da sauran masu alhaki a kan lamarin mafita ɗaya kafin wahala ta kai yan Najeriya bango.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262