Zamu Gudanar da Zabe Dun da Tashe-Tashen Hankula Kan Karancin Naira, INEC

Zamu Gudanar da Zabe Dun da Tashe-Tashen Hankula Kan Karancin Naira, INEC

  • Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce abubuwan dake faruwa ba zasu dakatar da zabe mai zuwa ba
  • Ana fargabar yanayin da ƙasa ke ciki na zanga-zanga a wurare da dama kan karancin naira ka iya kawo cikas ga shirin zaɓe
  • Abinda za'a jira a gani shi ne yadda INEC zata shirya zaben shugaban kasa nan da kwanaki shida masu zuwa

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ƙara tabbatar da cewa zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya zasu gudana yadda aka tsara duk da halin da ake ciki.

Tun bayan sauya fasalin takardun N200, N500 da N500, wanda babban banki CBN ya yi, da yawan 'yan Najeriya sun wayi gari cikin kunci da wahala wajen neman sabbin kuɗin.

Farfesa Mahmud Yakubu.
Zamu Gudanar da Zabe Dun da Tashe-Tashen Hankula Kan Karancin Naira, INEC Hoto: INECNigeria
Asali: Twitter

Sakamakon haka ne wasu ke fargabar zai wahala zaɓen ya yuwu, ko dai a ɗaga ko kuma a samu tasgaro duba da yadda karancin naira ya haddasa zanga-zanga a wasu sassan ƙasar nan.

Kara karanta wannan

"Muhimman Abu 5" Abinda Atiku Ya Bayyana Wa Yan Najeriya a Wurin Kamfen PDP Na Karshe Gabanin Zabe

Amma shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya kore fargabar da ake da cewa hukumar na aiki kafaɗa da kafaɗa da CBN da hukumomin tsaro, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"CBN ya bamu tabbacin ba za'a samu wani cikas ba ta ɓangarensa kuma a yanzu babu wasu matsaloli game da lamarin. Game da abinda ke faruwa a kasa na zanga-zanga, batu ne na tsaro."
"Hukumomin tsaro sun ƙara jaddada bamu tabbacin zasu samar da tsaro domin gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali, don haka bamu da wata damuwa game da wannan."

- Farfesa Mahmud Yakubu.

Ku sa kishin ƙasa a gaba - Yakubu

Ciyaman din INEC ya kuma bukaci matasa masu bautar kasa da zasu yi aikin wucin gadi su sa Najeriya da 'yan Najeriya a zuƙatansu, kar su kuskura su bi wani ɗan siyasa, a cewar rahoton Guardian.

Kara karanta wannan

Saura Mako 1: IGP Alkali Ya Jagoranci Atisayen Harbi Ana Cikin Shirye-Shiryen zaɓe

Ya gargaɗe su da cewa ko mai zai faru kar su yi gangancin barin na'urar tantance masu kaɗa kuri'a BVAS a hannun wani mutum na daban. Ya ce za'a bi diddiginsu don ganin abinda ke wakana.

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya gargadi shugaban kasa kan abinda ke shirin faruwa sanadin ƙarancin naira

Gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike, ya ce matakin da shugaban kasa ya ɗauka na saɓa wa umarnin Kotun koli alama ce ta gayyato tashin hankali.

Har yanzun ana tataburza tsakanin gwamnoni da gwamnatin tarayya kan sabon tsarin CBN na sauya fasalin wasu takardun naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel