IGP Alkali Ya Jagoranci Atisayen Harbi Ana Cikin Shirye-Shiryen zaɓe

IGP Alkali Ya Jagoranci Atisayen Harbi Ana Cikin Shirye-Shiryen zaɓe

  • Yan Siyasa tare da mukarraban su daga ko ina na sashin Najeriya na cigaba da gangami domin neman kuri'un masu kada kuri'a
  • Daidai lokacin yan sanda na shirin tabbatar da an gudanar da zaben cikin zaman lafiya ba tare da tashin-tashina ba
  • Masana na ganin zaben da za'a gudanar bana ka iya zama mafi fice a tarihin siyasar Najeriya

Abuja - A yayin da babban zaɓen Najeriya yake ƙara tunkarowa, an hangi shugaban ƴan sandan Najeriya Usman Alkali Baba da wasu manyan jami'an ƴan sanda na gumu wajen ɗaukar horon harbin bindiga domin shirin kota-kwana da ujila.

Atisayen dai ya faru ne yau sabar a filin ɗaukar horon harbi dake unguwar Deidei ta Abujan Najeriya.

Shugaban Yan Sandan Na Najeriya ya Nuna Kwarewa Wajen Atisayen daya gudana yau a Abuja
Babban Sufetan Ƴan Sanda na Ƙasa Ya Ɗauki Atisayen Harbi Domin Shirye Shiryen Gabatowar Zaɓe Hoto: Facebook/Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Da suke maida martani a wani hoto da shafin hukumar yan sanda ta ƙasa ya wallafa a sahar facebook, yan Najeriya sun jinjinawa ƙoƙarin tare da yabon Alƙali Usman Alkali Baba duba kwanaki 7 suka rage a shiga babban zaɓe a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Yi Halinta: An Gano Mutum 2 Da Suka Sauya Wa Buhari Tunani Kan Tawaita Wa'adin N500 da N100

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wanda hakan ka iya firgita gamida kawo wa masu ƙoƙarin lalata zaɓen matsala tare da cusa musu tunani da su sake salo.

Kuma Dai: An Kari Hari Ofishin Yan Sanda, An Kashe Jami'ai 3 Akalla

A wani labarin kuwa, ana saura kasa da mako guda zaben shugaban kasa an 2023, wasu yan bindiga sun kuma kai hari ofishin yan sanda a jihar Anambra, Kudu maso gabashin Najeriya.

Jihar Anambra ce mahaifar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Gregory Obi.

Wakilin Legit dake Anambra, Mokwugwo Solomon, ya bayyana cewa an kai wannan hari ne da sanyin safiyar Asabar, 18 ga watan Febrairu, 2023 ofishin yan sanda dake unguwar Ogidi, karamar hukumar Idemili North.

A cewarsa akalla jami'an yan sandan uku ne suka ce ga garinku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel