An Kashe Dan Wani Babban Jigon Jam'iyyar PDP A Legas, Dapo Sarumi

An Kashe Dan Wani Babban Jigon Jam'iyyar PDP A Legas, Dapo Sarumi

  • Wasu mutane dauke da bindigu sun harbe ɗan jigon PDP a Legas, Chief Dapo Sarumi har lahira da daddare
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa Mamacin tare da abokansa Shida na zaune da daddare ba zato maharan suka bude masu wuta
  • Hukumar yan sandan reshen jihar Legas ba tace komai ba zuwa yanzun duk da kiran da aka yi wa kakakinta

Lagos - Wasu yan bindiga da har yanzu ba'a gano su ba sun kashe Toyin Adeniji, ɗan kimanin shekara 47 a duniya kuma ɗa ga jigon jam'iyyar PDP a jihar Legas, Chief Dapo Sarumi.

Vangaurd ta rahoto cewa maharan sun harbe Toyin Adeniji har lahira ranar Litinin da daddare a gaban layin Sarumi Oyewole dake kallon kallo da gidan Mista Sarumi a Agege.

Taswirar jihar Legas.
An Kashe Dan Wani Babban Jigon Jam'iyyar PDP A Legas, Dapo Sarumi Hoto: vanguard
Asali: UGC

A cewar mutanen Anguwar marigayi Toyin na zaune tare abokanansa Shida a wurin dake kallon gidan jigon PDP da misalin karfe 9:00 na dare sa'ilin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Ana Halin Karancin Naira, Yan Bindiga Sun Aikata Mummunan Ta'adi a Abuja, Rayuka Sun Salwanta

Wani mazaunin yankin, wanda baya son sunansa ya fita, ya bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A ranar da abun ya auku, Adeniji da wasu abokansa na zaune a wurin dake kallon gidan Sarumi, kwatsam maharan fuskarsu a rufe suka wuce ta wurin ba zato suka dawo suka buɗe wuta."

Mutumin ya ƙara da cewa ganin ba lafiya, baki ɗaya waɗanda ke zaune suka ari na kare amma Adeniji bai samu sa'a kamar saura ba domin sun harbe shi a kai nan take rai ya yi halinsa.

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

A halin yanzu, Jami'an yan sanda sun kewaye wurin baki ɗaya duk da an ce an kai batun sashin binciken aikata muggan laifuka na jiha (SCIID), kamar yadda Punch ta rahoto.

Duk wani yunkuri na jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin, bai yi nasara ba domin be ɗaga kiran salula ba kuma bai turo amsar sakonni ba.

Kara karanta wannan

Shin Mutane Sun Yi Asara Kenan? Matakai 3 da Zaku Bi Ku Maida Tsoffin Naira Banki Duk da Wa'adi Ya Cika

A wani labarin na daban kuma Yan Bindiga Sun Harbi Shugaban Jam'iyyar PDP Na Gunduma a Jihar Imo

An tattaro cewa jigon siyasan ya shiga gida da misalin ƙarfe 9:00 na dare ba tare da sanin maharan sun yi masa kwantan ɓauna ba.

Wata majiya ta sanar da cewa nan take aka gaggauta tafiya da shi Asibiti saboda raunukan da ya ji sakamakon harbin da aka masa a kafafuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel