Labarin Su Ummitah da Abdul Karya Ne, Gidan Cin Abinci Na Gusto Ya Magantu

Labarin Su Ummitah da Abdul Karya Ne, Gidan Cin Abinci Na Gusto Ya Magantu

  • Labari ya karade kafar Twitter na yadda wsau 'yan mata suka so yiwa wata matashi kisan gwani a gidan cin abinci
  • Gidan cin abinci na Gusto ya karyata labarin da ke cewa an rike 'yan matan saboda sun ci abinci saurayin ya fece
  • Dambarwar Ummitah, Siyama da Abdul dai na ci gaba da daukar hankali a kafafen sada zumunta

Jihar Kano - Gidan cin abinci na Gusto a Kano ya bayyana gaskiya game da labarin d ake yawo cewa, ya kama wasu kwastomominsa saboda sun ci abinci sun gaza biya.

Idan baku manta ba, a makon nan ne wani labari ya yi shuhura a Twitter, na wani matashin da ya debi budurwarsa da kawayenta zuwa Gusto domin kodimo a ranar masoya, amma aka samu tsaiko.

Kara karanta wannan

Bidiyon Bidloniyan Najeriya Yana Rabawa Matasa $100 Kowannensu Ana Tsaka da Matsalar Kudi

A labarin da ya bayar a shafinsa na Twitter, saurayin ya ce ya sha mamakin yadda 'yan matan suka ci abincin da ya fi karfin shirin aljihunsa na wannan ranan.

Yadda Gusto ya karyata labarin Ummita da Abdul
Labarin Su Ummitah da Abdul Karya Ne, Gidan Cin Abinci Na Gusto Ya Magantu | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewarsa, sun lashe abincin gida da na kasashen waje na sama da N200,000, lamarin da ya sa ya cike wandonsa da iska ya fece a guje.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba gaskiya bane, kirkirarren labari ne

Sai dai, da gidan cin abincin ke bayani, ya ce sam hakan bai faru ba, kuma kowa na iya biyan kudin abinci a gidan.

A wata gajeriyar sanarwa da gidan cin abincin na Gusto ya fitar, ya ce:

"Muna son jan hankalin jama'a cewa labarin da yake ta yawo game mu wai mun kama wasu kwastomominmu saboda basu iya kudi ba bai faru ba.
"Wannan tsagwaron labarin karya ne. Gidan cin abincinmu na da yalwataccen jadawalin cin abin da kowa zai iya dauka."

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Matashi Ya Je Banki Da Ruwa a Bokiti, Ya Yi Wanka Yayin da Mutane Ke Kallonsa a Bidiyo

Ya zuwa yanzu dai matashin da 'yan matan basu fito sun musanta ikrarin Gusto ba, kana Gusto bai ambaci suna ba.

Yadda Abdul ya fece bayan 'yan mata sun ci abincin N220k

A baya kun ji yadda ta kaya tsakanin Abdul da 'yan matan da suka yiwa budurwarsa rakiya zuwa gidan cin abinci a Gusto.

Ya bayyana cewa, a zuwan farko suka ci abincin N155,000 inda shi kuwa ya ci na N8000 kacal a cikin gidan cin abincin.

Ya bayyana kaduwa da lamarin tun farkon da ya dauko 'yan matan, amma ya samu sanadiyyar guduwa nan take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel