Labari Mai Dadi: Bankuna Sun Ci Gaba da Karban Tsoffin N500, N1000

Labari Mai Dadi: Bankuna Sun Ci Gaba da Karban Tsoffin N500, N1000

  • Bayanai sun nuna cewa wasu bankunan kasuwanci a Najeriya sun yi fatali da sanarwan CBN kan daina karban N500 da N1000
  • Babban bankin Najeriya ya fitar da sanarwa jiya cewa bai umarci bankuna su ci gaba da amsar kuɗin ba kamar yadda ake yaɗawa
  • Hakan dai ta faru ne bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya tabbatar da haramcin takardun naira guda 2

Bankunan kasuwanci da ake ajiyar kuɗi sun bijirewa umarnin babban bankin Najeriya (CBN) sun ci gaba da karɓan tsoffin N500 da N1000 da aka haramta.

Wannan mataki da suka ɗauka ya saɓa wa sanarwar da CBN ya fitar jiya cewa ko kaɗan bai umarci bankuna su ci gaba karɓan tsoffin takardun naira daga hannun mutane ba.

Tsoffin takardun naira.
Labari Mai Dadi: Bankuna Sun Ci Gaba da Karban Tsoffin N500, N1000 Hoto: CBN
Asali: Twitter

Wane bankuna ne suka yi fatali da sanarwan CBN?

A rahoton jaridar Vanguard, bankunan da suka sa kafar wando ɗaya da CBN wajen karban tsohon kuɗin sun haɗa da G.T. Bank, First Bank, Fidelity Bank, da kuma Sterling Bank.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bamu Yi Umurnin Mayar Da Tsaffin N1000 da N500 Kowani Banki Ba, CBN

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, saɓanin sanarwan babban bankin, shafin yanar gizo-gizo da CBN ta samar domin maida tsoffin kuɗin ya umarci mutane su tafi bankunan kasuwanci su kai tsoffin N500 da N1000.

Sai dai a bayanan da shafin ya ƙunsa, ya gindiya sharadin cewa adadin kuɗin da mutane ke da damar kaiwa bankuna a yanzu ba zai wuce N500,000 ba.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wannan na zuwa ne bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jaddada cewa tsoffin N500 da N1000 sun tashi aiki tun 10 ga watan Fabrairu.

A jawabin kai tsaye ranar Alhamis 16 ga watan Fabrairu, shugaban ƙasan ya umarci CBN ya bar tsohon N200 ya ci gaba da yawo hannun yan Najeriya domin rage masu raɗaɗi.

Punch ta ce matakin Buhari ya haddasa cece-kuce sakamakon saɓa wa hukuncin Kotun koli, wanda ya ce a ci gaba da amfani da tsoffin kuɗin har zuwa lokacin da zata yanke hukuncin ƙarshe.

Kara karanta wannan

Karancin Kuɗi: Da Gangan Emefiele Yake Yaƙar APC - Gwamnan APC Ya Ɗau Zafi

Kana Shirin Gayyato Mana Rashin Bin Doka, Wike Ya Sake Tura Sako Ga Buhari

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya soki matakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na haramta tsoffin naira

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bukaci shugaban kasa ya girmama umarnin Kotun koli game da tsoffin kuɗi a Najeriya.

A cewar Wike saba wa hukuncin Kotu mai daraja ta ɗaya a Najeriya tamkar gayyato tashin hankali ne da rashin bin doka da oda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel