An Jefa Yan Najeriya Cikin Rudani: Gwamnan CBN Yace Bai Ce a Kai Tsaffin Kudade Kowani Banki Ba

An Jefa Yan Najeriya Cikin Rudani: Gwamnan CBN Yace Bai Ce a Kai Tsaffin Kudade Kowani Banki Ba

  • Babban bankin Najeriya ya karyata maganar cewa ya canza shawara kan lamarin mayar da tsaffin kudin N1000 da N500 bankuna
  • Dubunnan yan Najeriya sun dira ofishohin CBN yau don mayar da tsaffin kudadensu bayan jawbain Buhari
  • Gwamnoni akalla 10 sun ja layin daga da shugaban kasa inda wasu suka fara yi masa bore

Abuja - Babban bankin Najeriya CBN ya karyata labarin cewa ya umurci dukkan bankunan Najeriya su fara karban tsaffin kudaden N1000 da N500 daga hannun jama'a yanzu.

Kun ji rahoton cewa bankin ya canza shawarar kan mayar da kudi kowa ya kai CBN kadai.

Jawabin wanda har bankuna sun fara sanar da kwastamominsu su kawo kudi ya karade kafafen yada labarai.

Har aka ruwaito Diraktan Sadarwa na bankin, Osita Nwanisobi, da tabbatar da labarin.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Rikici Ya Barke A Jihar Legas Kan Lamarin Daina Karancin Naira

Kusan dukkan kafafen yada labaran Najeriya sun dauki labarin.

Kwatsam Osita Nwanisobi ya fitar da sabon jawabi cewa wannan labari ba gaskiya bane, bankin bai sanar da hakan ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A sabon jawabin da ya fitar shafin bankin na Tuwita, Osita yace:

"Bankin CBN ya samu labarin boge cewa CBN tayi umurni ga Bankuna su fara karban tsaffin N500 da N1000."
"Don fayyace gaskiya kuma bisa umurnin shugaban kasa a jawabinsa na 16 ga Febriaru, 2023, umurnin da CBN tayi kawai shine na fitar da tsaffin N200 na tsawon kwanaki 60 zuwa ranar 10 ga Afrilu 2023."
"Saboda haka mutane su yi watsi da wani labarin da ba CBN ya fitar ba,"

Asali: Legit.ng

Online view pixel