Emefiele Yaƙar Jam'iyyar APC Yake Yi -Gwamnan APC Ya Fusata

Emefiele Yaƙar Jam'iyyar APC Yake Yi -Gwamnan APC Ya Fusata

  • Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana gwamnan babban bankin Najeriya, a matsayin mai adawa da jam'iyyar APC
  • Gwamnan yace ko kaɗan Emefiele bai damu da halin da ƴan Najeriya suka tsinci kan su ba a dalillin sauya fasalin kuɗi
  • Masari ya nuna damuwar sa kan yadda gwamnan na CBN yake cigaba da bijerewa umurnin kotun ƙoli

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, yace abinda gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) yake yi domin aiwatar da shirin sauya fasalin kuɗi a ƙasar nan, yaƙi yake yi da APC. Rahoton Daily Trust

A cewarsa:

“Emiefiele kai ɗan adawar APC ne. Hakan ya nuna kwata-kwata baka san ƙasar nan ba saboda baka san halin matsin da ƴan Najeriya ke ciki ba saboda kana daga zaune cikin ofishinka kake aiwatar da wannan tsarin."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamna Wike Ya Yi Magana Ta Karshe Kan Yuwuwar Sulhu da Atiku Ana Dab da Zaɓen 2023

Masari
Emefiele Yaƙar Jam'iyyar APC Yake Yi -Gwamnan APC Ya Fusata
Asali: Facebook

Gwamnan yayi wannan furucin ne ranar Laraba a Katsina lokacin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyoyin ƴan kasuwar na jihar lokacin da suka je shigar da koken su kan ɗumbin asarar da zasu tafka idan aka daina karɓar tsofaffin kuɗi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Masari, wanda tunda farko ya umurci ƴan kasuwa da su cigaba da karɓar tsofaffin kuɗin bayan umurnin kotun ƙoli, ya nuna kaɗuwar sa kan yadda gwamnan babban bankin ya ƙi bin umurnin kotu.

"Saboda na kiran kwantirolan CBN na Katsina, ya gaya min cewa bai samu wani umurni ba daga hedikwatar su. Na tuntuɓi manajojin banki, ba a basu wani umurni ba daga hedikwata, CBN bata tuntuɓe su ba kwata-kwata."
“Sannan kuma Antoni Janar na tarayya ya bayyana cewa gwamnatin zata mutunta hukuncin kotu. Meyasa gwamnan babban bankin Najeriya ya ƙi bin umurnin kotu." Inji Masari

Kara karanta wannan

Jerin Riba 7 Da Muka Samu Dalilin Sauya Fasalin Takardun Kuɗi -Shugaba Buhari

Ƙarancin Naira: Ku Guji Tashin Hankali, Ku Nuna Fushinku a Zaben Shugaban Kasa, Kwankwaso Ga Yan Najeriya

A wani labarin na daban kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, ya bayyanawa ƴan Najeriya abinda yakamata suyi maimakon tayar da hankula kan ƙarancin kuɗi.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya nemi ƴan Najeriya da su huce fushi da ɓacin ran da aka jefa su a ciki idan lokacin kaɗa ƙuri'a yayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel