Shugaba Buhari Ya Gana da Godwin Emefiele Bayan Kotun Koli Ta Dage Zama

Shugaba Buhari Ya Gana da Godwin Emefiele Bayan Kotun Koli Ta Dage Zama

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sake gana wa da gwamnan babban banki CBN, Godwin Emefiele, a fadarsa dake Abuja
  • Ganawar ta zo ne awanni bayan Kotun koli ta ɗage zaman sauraron ƙara kan naira zuwa 22 ga watan Fabrairu, 2023
  • Kaduna, Kogi da Zamfara ne suka kai ƙarar FG da CBN daga baya wasu jihohin suka shiga don ganin an ƙara wa'adi

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, awanni kaɗan bayan Kotun koli ta ɗage zaman shari'a kan sauya fasalin naira.

A ɗazu Kotun Koli ta ɗage zaman sauraron shari'ar da gwamatocin jihohi suka shigar gabanta suna kalubalantar tsarin sauya fasalin naira da CBN ya ɓullo da shi zuwa 22 ga watan Fabrairu.

CBn da Buhari.
Shugaba Buhari Ya Gana da Godwin Emefiele Bayan Kotun Koli Ta Dage Zama Hoto: FG, CB
Asali: Facebook

Babban mai taimakawa shugaban kasa kan al'amuran yaɗa labarai da Midiya, Mallam Garba Shehu, ya tabbatar da ganawar Buhari da Emefiele ga Channels tv.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Buhari Ya Canza Shawara, FG Da CBN Zasu Duba Yuwuwar Tsawaita Wa'adin Naira

A cewarsa, gwamnan CBN na tsammanin ganin shugaban ƙasa kuma yana da yaƙinin manyan shugabannin biyu sun haɗu bayan taron majlaisar zartaswa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwana 11 da suka shige, shugaban kasan ya roki yan Najeriya su ba shi mako guda zai shawo kan matsalar karancin sabbin takardun naira da ta jefa su cikin wahala.

Ya nemi haka ne bayan ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta bukaci shugaban ya amince sabbi da tsofaffin N200, N500 da N1000 su ci gaba da yawo hannun mutane domin rage raɗaɗin da ake ciki.

Sai dai wata jita-jita da ke yawo ta yi ikirarin cewa Buhari na shirye-shiryen ƙara wa'adin amfanin tsohon kuɗin da watanni biyu, kakakin shugaban ya ce ba shi da ikon tabbatarwa ko musanta rahoton.

Tun da fari, Kotun koli ta yi umarni a ranar 8 ga watan Fabrairu, 2023, inda ta dakatar da gwamnatin tarayya da hukumominta daga haramta amfani da tsohon naira ranar 10 ga wata.

Kara karanta wannan

2023: Buhari Ya Zaba Ya Darje Tsakanin Atiku da Tinubu, Ya Faɗi Wanda Zai Share Hawayen Yan Najeriya

Buhari na duba yuwuwar kara watanni

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Amsa Kira, Zai Kara Wadataccen Wa'adin Amfani da Tsohon Kuɗi

Wasu rahotanni da suka fito ta bayan fage sun bayyana matsayar da aka cimma yayin ganawar shugaban ƙasa da gwamnonin Najeriya.

An tattaro cewa Buhari ya amince zai ƙara watanni amma bisa sharaɗin sai bayan gwamnoni sun janye ƙarar da suka shigar gaban Kotun ƙoli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel