Fatarta Kamar Madara: Bidiyon Yar Najeriya Mai Shekaru 150 Ya Yadu

Fatarta Kamar Madara: Bidiyon Yar Najeriya Mai Shekaru 150 Ya Yadu

  • An gano wata tsohuwa yar Najeriya wacce aka ce shekarunta ya kai 150, kuma mutane sun cika da mamakin ganin bidiyonta a TikTok
  • Yanayin matar da kyawun fatar jikinta ya haddasa cece-kuce a tsakanin matasa a manhajar TikTok
  • Wata matashiya mai suna Joy Peters wacce ta kai mata ziyara dauke da sha-tara ta arziki a daidai lokacin da ake fama da rashin wadatar naira ita ce ta wallafa bidiyon

An gano wata tsohuwa wacce ke cikin kyakkyawan nauyi duk da cewar ta kai shekaru 150 a duniya a nan Najeriya.

Wata matashiya wacce ke jagorantar gidauniyar Joy Peters da kuma tallafawa narasa karfi ta kai wa tsohuwar ziyara.

Yar Tsohuwa
Fatarta Kamar Madara: Bidiyon Yar Najeriya Mai Shekaru 150 Ya Yadu Hoto: @joypeterfoundation01
Asali: TikTok

A wani bidiyo da aka wallafa a TikTok, an gano matar zaune tare da diyarta a wani dan karamin gida.

Kara karanta wannan

Gamon Katar: Yar Najeriya Da Ke Aikin Kanikanci Ta Koma UK Da Zama, Ta Yi Fes Da Ita a Bidiyo

Abun da ya ba mutane da dama mamaki shine cewa har yanzu tana da kwarinta kuma mutum na iya gano tsantsar kyawunta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani babban abun daukar hankali game da tsohuwar shine yadda fatar jikinta ke sheki. Mutane da suka kalli bidiyon sun ce fatar jikinta ya yi tamkar madara.

Joy ta ziyarci matar ne bayan samun labarinta da kuma yadda take rayuwa a yanayi mara kyau.

Ta kuma kaiwa matar sha-tara ta arziki da suka hada da shinkafa da sauran kayan abinci.

Tsohuwar ta dan taka rawar jin dadi bayan kayayyakin sun isa gareta.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Cynthia ta ce:

"Tsohuwar nan ta zuba kyau lokacin da take matashiyar budurwa. Kalli fatar jikinta kamar madara."

@Habibtykayanmata ta yi martani:

"Dan Allah a wace jihar?"'

@Manchiee ta ce:

Kara karanta wannan

Zabin Allah Na Bi: Bidiyon Soyayya Da Wata Kyakkyawar Mata Da Mijinta Mai Nakasa Ya Tsuma Zukata

"Allah ya albarkace ki yar'uwa."

@princess ceeta yi martani:

"Allah ya ci gaba da yi maki albarka."

@user548124101206 ya ce:

"Allah ya yi maki albarka, mama."

@Momtwins ta ce:

"Allah ya yi maki albarka da ahlinki."

Shine zabin da Allah ya yi mani, matar aure ta nuna tsananin son da take yi wa mijinta mai nakasa

A wani labarin, wata matar aure ta tabbatar da lallai har yanzu akwai soyayya ta gaskiya bayan ta wallafa bidiyonta tare da mijinta mai nakasa. An gano ta tare da mijinta suna zuba soyayya cike da shaukin junansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel