Ribar 7 Da Aka Samu a Dalilin Sauya Fasalin Takarɗun Kuɗi -Shugaba Buhari

Ribar 7 Da Aka Samu a Dalilin Sauya Fasalin Takarɗun Kuɗi -Shugaba Buhari

  • Duk da matsalolin da tsarin sauya fasalin kuɗi ya haifar, shugaba Buhari yace tsarin ya haifar da ɗa mai ido.
  • Shugaban ƙasar yace kuɗaɗen da basa zuwa bankuna a baya, yanzu sun koma hannun bankuna
  • Shugaba Buhari ya kuma lissafo wasu ribobin da ƴan Najeriya zasu samu a dalilin sauya fasalin kuɗin

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa shirin sauya fasalin takardun naira ya haifar da ɗa mai ido, duk da cewa an samu wasu matsaloli wajen aiwatar da shi.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi ga yan Najeriya, kan ƙara wa'adin tsofaffin kuɗi, a safiyar Alhamis, 16 ga watan Fabrairun 2023.

Buhari
Ribar Da Aka Samu a Dalilin Sauya Fasalin Takarɗun Kuɗi -Shugaba Buhari
Asali: UGC

Shugaban ƙasar yace tun bayan da aka fara aiwatar da shirin, kusan takardun kuɗi waɗanda yawan su ya kai na naira tiriliyan 2.1, waɗanda ke a hannun mutane aka mayar da su zuwa bankuna.

Kara karanta wannan

Duk Wanda Ya Cinyemun Kuɗi Kuma Ya Ƙi Zaɓena Zai Sheƙa Barzahu, Ɗan Takarar PDP a 2023

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan na nufin kaso 80% na kuɗaɗen da basu a cikin bankuna a da, yanzu sun koma banki.

Shugaban ƙasar ya lissafo tagomashin da Najeriya zata samu a dalilin sauya fasalin kuɗin.

Ga su nan ƙasa kamar haka:

a. Ƙara ƙarfin matakan da muka ɗauka kan tattalin arziƙi.

b. Rage yawan kuɗaɗen dake yawo wanda hakan zai sanya farashin kayayyakin gida ya sauka.

c. Samun sauƙin hauhawan farashi a dalilin ƙarancin kuɗin dake yawo wanda hakan zai sanya hauhawan farashi ya sauka.

d. Ɗurƙushewar duk wasu haramtattun harkokin kasuwanci wanda hakan zai taimaka wajen daƙile cin hanci da samun kuɗi ta haramtattun hanyoyi.

e. Daidaituwar farashin naira a kasuwar canjin kuɗi.

f. Samuwar ƴan ƙananan basussuka da rage kuɗin ruwa.

g. Ƙaruwar gaskiya a wajen ɗaukar matakan tattalin arziƙi wanda hakan zai tabbatar an aiwatar da dokokin yaƙi da kuɗaɗen haram.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamna Wike Ya Yi Magana Ta Karshe Kan Yuwuwar Sulhu da Atiku Ana Dab da Zaɓen 2023

Dalilai 5 Da Yasa Muka Kawo Tsarin Sauya Fasalin Naira: Buhari Da Safiyar Yau

A wani labarin na daban kuma, shugaba Buhari ya bayyana wasu muhimman dalilai da suka sanya gwamnatinsa ta kawo tsarin sauya fasalin takardun kuɗi.

Shugaba Buhari yace bayyana dalilan ga ƴan Najeriya a zamo wajibi duba da yaddda lamarin ya tsananta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel