Bidiyon Yadda Wasu Mata Suka Dunga Yi Wa Amarya Kallon Uku Saura Kwata a Wajen Bikinta Ya Yadu

Bidiyon Yadda Wasu Mata Suka Dunga Yi Wa Amarya Kallon Uku Saura Kwata a Wajen Bikinta Ya Yadu

  • Wata kyakkyawar amarya ta cika da farin ciki yayin da take taka rawa a ranar bikinta duk da kallon banzar da yan biki suka dungi yi mata
  • Amaryar wacce ke sanye da kayan saki da dogon takalmi,ta ci gaba da harkokin gabanta yayin da mutane da dama suka yi jugum-jugum suna kallo
  • Yan Najeriya da dama da suka yi martani kan bidiyon sun yi mamakin dalilin da yasa bakin bikin suka hallara idan har basa son auren

Wani bidiyo da @simplykiajamal ya wallafa ya nuno lokacin da wata amarya ke taka rawa cike da farin ciki a yayin shagalin bikinta.

Kewaye da yan biki, amaryar sanye da dogon takalmi tana ta rausayawa daidai da sautin kidin da ke tashi. Matan da ke kusa da ita sun yi kicin-kicin da fuska yayin da masu amfani da TikTok suka yi wa abun fassara daban.

Kara karanta wannan

Zabin Allah Na Bi: Bidiyon Soyayya Da Wata Kyakkyawar Mata Da Mijinta Mai Nakasa Ya Tsuma Zukata

Amarya a taron mata
Bidiyon Yadda Wasu Mata Suka Dunga Yi Wa Amarya Kallon Uku Saura Kwata a Wajen Bikinta Ya Bayyana Hoto: @simplykiajamal
Asali: TikTok

Amarya na rawa sanye da dogon takalmi

Duk da yanayin fargabar da wajen ke ciki, amaryar ta ci gaba da kwasar rawanta, Mutane da dama sun yi mamakin ko dai mutanen basa farin ciki da auren nata ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu mutanen da ke wajen sun share kamarar wayarsu don daukar hadadden bikin.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

prettyfacehilda ta ce:

"Shin basa taya yar'uwarsu farin ciki ne?"

estherowusuaa163 ta ce:

"Duk da yanayin fuskokinsu, bata damu ba ko kadan. Na so karfin gwiwarta ba mu ga kowa ba kawai."

Tammy Cummings ta ce:

"Wa ya tilasta masu zuwa su zaune ne a wajen."

Queens Love937 ta ce:

"Bana son yanayin yadda suke kallonta."

ojukotimi123 ta ce:

"Za mu ce ta fi su ilimi kuma ta auri mutum mai kudi saboda ban san dalilin da yasa basa son ta ba."

Kara karanta wannan

Bayan Zaman Kotun Koli, CBN Ya Sake Magana Kan Masu Sayar da Sabbin Naira

Mrs morina ta ce:

"Kai menene dalilin da yasa suke kallon amaryar haka."

Bidiyon yadda matar aure ta nunawa mijinta mai nakasa kauna ya burge jama'a

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata matar aure ta nunawa duniya irin so da kaunar da take yi wa mijinta mai nakasa ba tare da la'akari da yanayinsa ko abun da mutane za su fadi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel