Dalilin da Yasa ni da El-Rufai Muka Halarci Zaman Kotu, Gwamna Yahaya Bello

Dalilin da Yasa ni da El-Rufai Muka Halarci Zaman Kotu, Gwamna Yahaya Bello

  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, tare da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna sun halarci zaman kotun koli a yau
  • Yayin zantawa da manema labari bayan zaman kotun, Bello yace sun halarci zaman ne saboda talakawan Najeriya
  • Gwamnan yace talakawan na cikin tsaka mai wuya saboda tsarikan babban bankin Najeriya na canza fasalin Naira

FCT, Abuja - Kotun koli Najeriya a ranar Laraba ta yi zama mara tsawo kan batun tsarikan musayar kudi da babban bankin Najeriya ke yi wanda gwamnoni suka kai gaban kotun.

Kotun Koli
Dalilin da Yasa ni da El-Rufai Muka Halarci Zaman Kotu, Gwamna Yahaya Bello. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Hallara gaban kotun a yau akwai gwamnoni Yahaya Bello na Kogi da Gwamna Nasir el-Rufai na jihar Kaduna tare da jerin lauyoyinsu, Channels TV ta rahoto.

Yayin jawabin bayan zaman kotun da aka dage zuwa ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu don sauraron cikakkeiyar karar da jihohi 10 suka kai, Gwamna Bello ya sanar da manema labarai cewa hsi da El-Rufai sun je ne don tabbatar da an yi wa talakawa da ke mawuyacin hali adalci.

Kara karanta wannan

"A Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudi Har Karshen Shekara": Kotun Kolin Najeriya Ta Yanke Hukunci

"Mun zo kotu ne saboda 'yan Najeriya da ke fama sakamakon sauya fasalin kudi da yadda babban bankin Najeriya yake son a koma amfani a kudi ba tsaba ba, shiyasa muke nan a yau."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Gwamnan yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel