Kai Tsaye: Yadda Shari’ar Gwamnoni da FG ke Gudana a Kotun Koli

Kai Tsaye: Yadda Shari’ar Gwamnoni da FG ke Gudana a Kotun Koli

A yau Laraba, 15 ga watan Fabrairun 2023 ne wasu gwamnonin Najeriya da Gwamnatin tarayya suka gurfana a gaban Kotun koli kan wa’adin da gwamnatin tarayya ta diba na daina amfani da tsofaffin takardun N200, N500 da N1000.

A makon da ya gabata ne Gwamnonin jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara suka maka gwamnatin tarayya gaban kolin inda wasu jihohi suka biyo bayansu a karar.

Kotu ta dage karar gwamnoni 12 da CBN zuwa 22 ga watan Faburairu

Bayan sauraran batutuwa da kuma kara adadin jihohin da ke kalubalantar gwamnati, kotun koli ya dage ci gaba da zaman zuwa ranar 22 ga watan Faburairu mai zuwa.

Kotun koli ta gama wasu jihohi 9 cikin masu kalubalantar yunkurin Buhari da CBN na sauyin Naira

Baya ga jihohin Kaduna, Zamfara da Kogi, kotun koli ya amince da shigar jihohi tara karar da aka shigar mai kalubalantar kudurin CBN na wa’adin daina amfani da tsoffin kudi.

Jihohin da kotun ya gama sun hada da Katsina, Legas, Ondo, Ogun, Ekiti, Sokoto, Bayelsa, Ogun da Edo.

Sai dai, sabanin kalubalanta, jihohin Bayelsa da Edo suna goyon bayan CBN ne da gwamnati, inda suka shiga batun a matsayin wadanda ake kara.

Manyan lauyoyi, gwamnoni sun hallara yayin da Justis John Okoro ke jagorantar kwamitin mutum 7

Kotun kolin Najeriya ta cika ta tumbatsa da manyan lauyoyin Najeriya, sauran lauyoyi da wasu daga cikin gwamnoni domin sauraron yadda za ta kaya a shari’ar da aka shigar kan manufar sauya kudi na Babban Bankin Najeriya (CBN).

Daga cikin gwamnonin da suka hallara akwai na jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da takwaransa na jihar Kogi, Yahaya Bello.

A zaman karshe da aka yi, kotun ta yanke hukuncin wucin-gadi inda ta dakatar da aiwatar da wa’adin 10 ga watan Fabrairu da CBN ya saka a matsayin lokacin daina amfani da tsoffin kudi na N200, N500 da N1,000.

Gwamnatocin jihohin Zamfara, Kogi da Kaduna sun shigar da kara a kan gwamnatin tarayya da CBN.

Sauran jihohin da suka nemi shiga shari’ar da ake yi da gwamnatin tarayya da CBN sun hada da Neja, Kano, Ondo da Ekiti.

An fara zaman kotun inda Justis John Okoro ke jagorantar wani kwamiti na mutum bakwai, Channels TV ta rahoto.

Ya ce bai kamata kotu ta yi watsi da shari’ar da manufarta ba kasancewar lamarin ya shafi mawuyacin halin da ‘yan Najeriya ke ciki.

Jihar Lagas, ta hannun Atoni Janar dinta, Moyosore Onigbanjo, ta nemi a saka ta a cikin shari’ar.

Jihar Bayelsa karkashin jagorancin Damian Dodo ma ta nemi shiga shari’ar a matsayin mai ba da bayani. Haka ma jihar Edo ta nemi shiga a wannan matsayin.

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng