Sauya Fasalin Naira: Kungiyar Dattawan Arewa ta Magantu, Ta Bayyana Irin Kwafsawar da Buhari Yayi

Sauya Fasalin Naira: Kungiyar Dattawan Arewa ta Magantu, Ta Bayyana Irin Kwafsawar da Buhari Yayi

  • Kakakin Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Hakeem Baba-Ahmed ya siffata sauyin fasalin naira a matsayin mataki mafi sauki da aka dauko wajen rushewar jam'iyyar APC gaba daya
  • Dattijon Arewan ya kara da cewa, babban abokin adawar APC ya yi amfani da wannan matakin ne don sawarwaro APC kasa warwas a gangamin zabe mai karatowa
  • Haka zalika, ya koka game da yadda Buhari ya nuna halin ko in kula, duk da tsananin rayuwar da talaka ke ciki, bayan ya gana da gwamnonin jam'iyyar APC amma har yanzu babu wani sakamako mai kyau daga gareshi

Kaduna - Mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Hakeem Baba-Ahmed, ya siffata sauyin fasalin Naira a matsayin babban matakin rushewar jam'iyyar APC.

Hakeem BabaAhmed
Sauya Fasalin Naira: Kungiyar Dattawan Arewa ta Magantu, Ta Bayyana Irin Kwafsawar da Buhari Yayi. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ahmed ya fadi hakan ne wannan Talatar yayin zantawa da Channels TV.

Kara karanta wannan

Matsayar Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi a kan batun Canjin N200, N500 da N1000

Inda ya ce, Buhari ya kwafsa, mambobin NEF din ya ce shugabancin a makwanni biyu da suka shude yayi nasarar tarwatsa bangeren tattalin arziki da karancin Naira.

A cewarsa, matsin rayuwar da dokar ta jawo na kokarin sawarwaro jam'iyya mai mulki kasa warwas a yankin arewacin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa, bai dace a ce babban abokin adawar APC ya dauki babban matakin rushewar jam'iyya mai mulkin ba.

Alamu na nuna shugaban kasa Muhammadu Buhari baya sauraron kowa duk da zai iya kawo karshen matsalar ta hanyar barin amfani da sabbi da tsoffin kudin gaba daya.

"Mun kai nan ne saboda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwafsa saboda yadda ya zura ido irin wannan tamarin na faruwa ana gab da zabe yayin da kake kamfen don ganin an zabi jam'iyyarka.

Kara karanta wannan

Buhari Bai Yi Kokari Sosai a Nan ba, Jigon APC Ya Fadi Bangare 1 da Tinubu Zai Gyara

"Wannan lamarin kudin shi ne babban matakin da zai sawarwaro jam'iyyar APC kasa warwas. Idan har babban abokin adawar APC ya shirya musu tuggun ganin sun sha kaye a zaben, bai da ce a ce ya dauki hanya mafi sauki ba na sauyin fasalin naira.
"Mutanensu na cewa an sauya fasalin ta ne don kayar da Tinubu, gwamnoni na cewa an sauya fasalin ne don ganin ya sha kaye. Shima 'dan takarar da kansa ya ce an yi hakan ne don a kayar dashi.
"Mutane su ne cikin yunwa - a zahiri, mutane na cikin yunwa. Babu kudi. A makwanni hudu da suka shude, kun rusu bangaren tattalin arziki zuwa daya, saboda babu kudi.
“Maganar gaskiya, mutane sun fusata, a halin da shugaban kasar ya nuna halin ko in kula ko ya gaza take wa Emefiele birki ta hanyar cewa, saurara, akwai zabi biyu na amfani da su tsawon watanni shida masu zuwa.”

Kara karanta wannan

Ba Gwamnan Arewan da Zai Iya Kawowa Tinubu Kuri'un Jiharsa, Tsohon Shugaban NHIS

- A cewarsa.

Premium Times ta rahoto cewa, Buhari ya gana da wasu gwamnonin jam'iyya mai mulki, inda ya ce a bashi kwanaki bakwai don ya dauki mataki kan karancin kudi. Har yanzu bai yi komai ba, sama da kwanaki 10 da yin alkawarin.

A makon da ya gabata, shugaban kasar ya gana da Majalisar Tarayya, inda majalisar ta umarci Babban Bankin Najeriya da ya buga gami da bada sabbin kudi isassu.

Bankuna Na kin karbar tsofaffin kudi duk da umarnin kotun koli

A wani labari na daban, bankuna a fadin kasar nan suna cigaba da kin karbar tsofaffin kudi duk da Umarnin kotun koli.

Sun sanar da cewa, basu samu umarnin karbar tsofaffin kudin ba daga babban bankin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel