Bankuna Sun yi Fatali da Umarnin Kotun Koli, Sun Daina Karbar Tsofaffin Kudi

Bankuna Sun yi Fatali da Umarnin Kotun Koli, Sun Daina Karbar Tsofaffin Kudi

  • Wasu bankunan ‘yan kasuwa da ke fadin jihohin Najeriya har da Abuja sun daina karbar tsofaffin takardun Naira
  • Sun bayyana cewa, ba su aka kai kotu ba, babban bankin Najeriya aka kai, don haka suna jiran umarnin babban bankin kafin cigaba da karba
  • Wasu jihohin Najeriya sun maka Gwamnatin tarayya a gaban kotu kan Sabon tsarin da ta kawo na sauya fasalin wasu takardun

Bankunan da ake zuba kudade a fadin kasan nan a jiya Litinin sun ki karbar tsofaffin takardun naira duk da umarnin kotun koli wacce ta tsawaita wa’adin daina karbarsu har zuwa 15 ga Fabrairu da za a dauka mataki.

Babban bankin Najeriya
Bankuna Sun yi Fatali da Umarnin Kotun Koli, Sun Daina Karbar Tsofaffin Kudi. Hoto daga channelstv.com
Asali: Facebook

Binciken Daily Trust a fadin jihohin Najeriya da babban birnin tarayya ya nuna cewa bankunan ‘yan kasuwa suna ta kin karbar kudin daga kwastomomi da suka shiga rassan don zuba kudin a asusunsu.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamnan CBN ya yi wata ganawar sirri da Buhari kan batun Naira

Idan za a tuna, kwamitin alkalai bakwai na kotun kolin a makon da ya gabata sun bada umarnin wucin-gadi wanda ya dakatar da shirin babban bankin Najeriya na daina amfani da tsofaffin takardun N200, N500 da N1,000.

Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Fabrairun 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan hukuncin ya biyo bayan karar da gwamnatocin jihohin Kogi, Kaduna da Zamfara suka kai don kalubalantar tsarin gwamnatin Shugaba Buhari na canza fasalin Naira.

Wannan cigaban ya bar ‘yan Najeriya masu tarin yawa cikin dimuwa. Yayin da wasu ke karbar tsofaffin kudi, wasu basu karba kwata-kwata.

A cikin wannan lamarin, Shugaba Buhari ya bukaci a bashi kwanaki bakwai domin samun damar shawo kan matsalar da karancin sabbin kudin and suka janyo amma har yanzu shiru.

Halin da ake ciki a jihohi

Kara karanta wannan

Gaskiya 3 Da Ya Kamata Ku Sani Game da Matsayin Tsoffi Da Sabbin Naira a Yanzu

Daily Trust ta ziyarci wasu daga cikin bankunan ‘yan kasuwa a Legas, Abuja, Kwara, Ondo da Bayelsa kuma ta ga ba a karbar tsofaffin takardun kudin.

“Na sha mamaki da ake kin karbar tsofaffin takardun kudin a bankuna a yau. Na kai kudin da nake da su amma banki sun ki karbar tsofaffin N500.”

- Juliet Okoro ta koka bayan ta ziyarci daya cikin bankunan ‘yan kasuwa da ke Ikeja.

Lamarin da ke faruwa kuwa a Bayelsa shi ne, kusan dukkan bankunan ‘yan kasuwa da ke Yenagoa, babban birnin jihar, sun daina aiki tare da garkamewa saboda barazanar tsaro.

Manyan ma’aikatan bankunan UBA, Jaiz da FCMB da suka hiranta da Daily Trust da bukatar a boye sunansu, sun tabbatar da wannan cigaban inda suka ce yawancin bankuna sun daina karbar tsofaffin kudin, sun ce suna jiran umarni daga CBN don daukar matakin gaba.

Keburan Talauci: Matashi ya bukaci a dawo masa da sadakarsa

Kara karanta wannan

An Samu Jihar APC ta 5 da ta Shigar da Karar Gwamnatin Buhari a Dalilin Canza Kudi

A wani labari na daban, wani matashi ya bukaci coci da su hanzarta biyansa duk kudin da ya saka sadaka.

Yace ya hakura da aljanna saboda tsabar talaucin da ya saka shi a gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel