CBN: Tsofaffin Takardun N200, N500 da N1000 Sun Daina Amfani a Najeriya

CBN: Tsofaffin Takardun N200, N500 da N1000 Sun Daina Amfani a Najeriya

  • Babban bankin Najeriya ya bayyana cewa tuni tsoffin takardun naira suka rasa martabar halascin kuɗi a Najeriya
  • Kwanturolan CBN na Bauchi, Haladu Idris Andaza, ya ce har yanzu yan Najeriya na da damar kai kuɗin banki a karɓa
  • A yan kwanakin nan yan Najeriya sun shiga ruɗani sakamakon rashin sanin ainihin wa'adin CBN

Babban bankin Najeriya (CBN) ya ayyana cewa tsoffin takardun naira da ya sauya N200, N500 da N1000 sun zama mara amfani tun ranar 10 ga watan Fabrairu, 2023.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa tun asali CBN ya zaɓi wa'adin 31 ga watan Janairu a matsayin ranar karshe ta ci gaban yawon tsoffin naira amma ya tsawaita wa'adin saboda matsin lamba daga 'yan Najeriya.

Sauya fasalin naira.
CBN: Tsofaffin Takardun N200, N500 da N1000 Sun Daina Amfani a Najeriya Hoto: CBN
Asali: UGC

Haka nan, kafin cikar wa'adin 10 ga watan Fabrairu, jihohin Kogi, Kaduna da Zamfara suka garzaya Kotun Koli, suka roƙi ta dakatar da CBN daga aiwatar da wa'adin.

Kara karanta wannan

Mafita Ta Samu: Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Sabbin Naira Na CBN

Legit.ng Hausa ta kawo maku rahoton yadda Kotun ta amince da buƙatar masu ƙara kana ta ɗage sauraron shari'ar zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu, 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tun bayan wannan hukuncin na Ƙotun koli, babban bankin ƙasa ya yi gum bai ce komai ba dangane da taƙamaiman lokacin haramta amfanin tsohon naira.

Sai dai wannan shiru na CBN ya jefa 'yan Najeriya cikin ruɗani da waswasi kan matsayin tsohon takardun naira, wanda wasu suka fara daina karɓa amma a wasu wuraren ana karɓa.

Wa'adi ya cika tun a 10 ga watan Fabrairu, 2023 - CBN

Da yake tsokaci kan ci gaban yayin hira da 'yan jarida, Kwanturolan CBN na jihar Bauchi, Haladu Idris Andaza, ya ce tsoffin takardun sun rasa martabar zama hastattun kuɗin naira.

"A cikin awanni 24 da suka gabata, mutane sun aiko mana da tambayoyi daga bangarori daban-daban kan matsayar mu kan tsoffin takardun naira."

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Tsohon Minista Adeyeye Ya Tsage Gaskiya, Ya Tono Abinda Gwamnan CBN Ya Jawo a Tarihin Najeriya

"Domin kore waswasi CBN ya shirya kuma kofa a bude take zai karbi tsoffin naira bisa wasu sharuɗɗa da ƙa'idoji."
"Kwastomomi na da damar kawo mana kuɗinsu rassan CBN wanda ba zasu yi ba hakan ba a bankunan kasuwanci saboda tsohon kuɗin sun zama marasa amfani tun 10 ga wannan watan."

Hanya ɗaya da 'yan Najeriya zasu tsira daga asarar tsohon kuɗi

Bugu da ƙari, kwanturolan ya ƙara da cewa 'yan Najeriya zasu iya kai tsoffin kuɗinsu rassan CBN a jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.

A rahoton Tribune, Idris Andaza ya ci gaba da cewa

"CBN na ganin mutane zasu kara samun natsuwa idan suka je rassan bankin da ke jihohin 36 da Abuja domin maida tsohon kuɗinsu cikin asusu. Akwai Fam da aka tanada a shafin ganar gizo na CBN kan sauya fasalin naira."
"Ana bukatar kowane kwastoma ya shiga ya cike Fam ɗin, bayan ka cike za'a baka wasu lambobi, wannan lambar zaka zo mana da ita bayanai na ciki. Za'a nemi ka ba da bayaninka, Asusu da yawan kuɗin da zaka aje."

Kara karanta wannan

Shin CBN Ya Kara Wa'adin Amfani da Tsoffin Kuɗi? Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani a Halin Yanzu

A wani labarin kuma Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya koka kan yadda mutane ke fama da ƙunci saboda tsarin sauya fasalin naira na CBN

Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya ce ya zama wajibi masu alhaki su gaggauta yaye wa yan Najeriya wannan wahalar wacce ta sa suka fara tunzura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel