'Yan Sanda Sun Kwamushe Faston da Aka Gani Yana Rataye da Bindiga AK-47 a Abuja

'Yan Sanda Sun Kwamushe Faston da Aka Gani Yana Rataye da Bindiga AK-47 a Abuja

  • Rundunar ‘yan sandan Abuja sun kama wani faston da aka ga rataya bindiga kirar AK-47 a wurin wani taron ibada
  • Kwamishinan ‘yan sandan Abuja ya nemi a dakatar da dan sandan da ya ba faston bindigarsa yayin da yake bakin aiki
  • A halin yanzu, ana tsare da malamin a hannun ‘yan sanda, ana ci gaba da bincike don duba yiwuwar daukar mataki na gaba

Garki, Abuja - Wani fasto, Uche Aigbe da aka gani a wani bidiyo a Abuja yana rataye da bindiga kirar AK-47 ya shiga hannun ‘yan sandan Najeriya, rahoton Punch.

Wannan na zuwa ne bayan da kwamishinan ‘yan sandan FCT, Sadiq Abubakar ya ba da shawari ga babban sufeton ‘yan sanda, Usman Baba kan a dakatar da dan sandan ya ba faston bindigan.

An ruwaito cewa, Sufeto Musa Audu, wani jami’in dan sanda da ke aikin tsaro ne ya dauki bindigar ya ba malamin yayin da ake taron a Abuja.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mataimakin Sufetan Yan Sanda Na Kasa, Lawan Jimeta, Ya Rasu, An Faɗi Abinda Ya Yi Ajalinsa

An kama fasto mai yawo da bindiga a coci
'Yan Sanda Sun Kwamushe Faston da Aka Gani Yana Rataye da Bindiga AK-47 a Abuja | Hoto: Punch Newspaper
Asali: Facebook

Majiya ta shaidawa jaridar cewa, a halin yanzu an tsare fasto Aigbe da dan sanda Audu a karkashin rundunar IRT da kuma cibiyar bincike ta ‘yan sanda ta Force Intelligence Bereau da ke Abuja a ranar Lahadi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda batun ya faro daga wurin taron ibada

A tun farko an ruwaito cewa, an ga faston da ke jagorantar shirin addinin kirista a House of the Rock ya shiga filin ibada dauke da bindiga a kafadarsa, wani rahoton na Punch.

‘Yan Najeriya da yawa ne suka dauki zafi, suka yi ta martani a kafar sada zumunta, inda wasu ke ganin bai dace malamin addini ya yi irin wannan fita ba.

Har mabiya bayansa a wurin taron, sun bayyana kaduwa da shiga wani yanayi bayan ganinsa da shigar da ba a saba ganin malamin addini na kirki ya yi ba.

Kara karanta wannan

Matasan APC sun yiwa Gwamna Mai Mala Buni rajamu a Yobe

An garkame cocin faston da ke ba da maganin bindiga

A wani labarin kuma, kun ji yadda gwamnatin Kogi ta umarci a garkame wani asibiti mai hade da coci inda ake ba da maganin bindiga.

Rahoton da muka sami ya bayyana cewa, ana ba da magani cikin rashin tsafta a asibitin, lamarin da ya jawo hankalin jama’a da ma gwamnati.

Ya zuwa yanzu dai an bincika an gano asibitin bashi da cikakkun kwarrarun likitoci da ke karbar haihuwa da kuma lasisin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel