Bankuna Da ’Yan Kasuwa Sun Fara Daina Karbar Tsoffin Kudade a Birnin Akure, Jihar Ondo

Bankuna Da ’Yan Kasuwa Sun Fara Daina Karbar Tsoffin Kudade a Birnin Akure, Jihar Ondo

  • Ma’aikatan banki sun bayyana shawari ga kwastomomi cewa, su fara kudadensu zuwa babban bankin kasa, CBN
  • ‘Yan kasuwa a jihar Ondo sun fara kin tsoffin kudade saboda gudun asarar da ka iya biyo bayan karbar kudaden
  • Wani kanti a Abuja ya daina karbar tsoffin kudi, ya ce ba zai jure daukar asara ba haka siddan ba tare da umarni ba

Akure, jihar Ondo - Wasu bankunan kasuwanci a birnin Akure na jihar Ondo sun fara kin karbar tsoffin kudaden N200, N500 da N1000.

Kwastomomi da yawa ne suka kai tsoffin kudadensu domin su ajiye, amma ma’aikatan bankunan suka ki karbar kudaden da suke tsoffi.

A bankin Jaiz, wani ma’aikacin bankin ya shawarci kwastomomin da su tattara tsoffin kudaden su kai Babban Bankin Najeriya (CBN).

Bankuna da 'yan kasuwa sun daina karbar tsoffin Naira
Bankuna Da ’Yan Kasuwa Sun Fara Daina Karbar Tsoffin Kudade a Birnin Akure, Jihar Ondo | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Wani ma’aikacin bankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, suna aiki ne daidai da umarnin babban bankin na CBN.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamnan CBN ya yi wata ganawar sirri da Buhari kan batun Naira

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran bankunan da jaridar The Nation ta ce ta ziyarta a Ondo sun hada da UBA, FCMB, First Bank da Zenith Bank.

‘Yan kasuwa ba sa karbar tsoffin kudi

A bangare guda, wasu ‘yan kasuwa sun fara kin tsoffin kudaden a daidai lokacin da ake ci gaba da kai ruwa rana kan batun karancin kudi.

Sun kafa hujja da cewa, bankuna sun ki karbar tsoffin kudaden, don haka babu yadda za a yi su karba su yi asara.

Wakilin Legit.ng Hausa a jihar Gombe ya ziyarci gidan mainLB da ke titin Bye Pass a jihar, inda aka ce ba za a karbi tsoffin kudi ba, kuma babu batun tiransfa.

A cewar mai matsa mai, hukumar gidan basu amince a karbi tsoffin kudin ba, kuma dole sai dai a yi amfani da POS idan ta kama.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kasa ta birkice, 'yan Najeriya sun fara zanga a hedkwatar CBN bayan hukuncin kotu

Duk wannan dai na zuwa ne a gefen umarnin kotun koli na cewa a ci gaba da kashe tsoffin kudi hade da sabbi har zuwa ranar 15 ga watan Janairun 2023.

Gwamnonin Arewacin Najeriya ne suka maka gwamnatin tarayya a kotu tare da neman a kara wa’adin daina a amfani da tsoffin kudade a kasar.

Kantin Abuja ya daina karbar tsoffin kudi

A wani labarin kuma, kun ji yadda wani katafaren kantin siyayya a Abuja ya bayyana daina amfani da kuma karbar tsoffin takardun Naira.

Katin na H-Medix ya lika wata takardar sanarwar da ke bayyana kin N200, N500 da N1000 tsoffi duk kuwa da umarnin kotu a ci gaba da amfani da kudaden.

Kantin ya ce, bai samu sanarwar a hukumance da ke cewa a ci gaba da amfani da tsoffin kudi ba, don haka ba zai tafka asara ta hanyar karbar kudaden ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.