An Damke Mutumin da Yayi Fashi a Coci, Dauke da Kayan da ya Kwasa

An Damke Mutumin da Yayi Fashi a Coci, Dauke da Kayan da ya Kwasa

  • 'Yan agajin kungiyar tsaro ta Amotekun sun yi ram da wani mutumi da kayan sata bayan ya yi fashi a wata majami'a
  • Mr Adewinmbi ya ce an kama mutumin da ake zargi da na'urar daukar murya, na'urar kara karfin murya, ganguna da sauran kayayyaki
  • Mazauna yankin sun yi kiran gaggawa ga 'yan agajin Amotekun kan yadda suke zargin mutumin mai shekaru 47 da balle majami'ar, wanda hakan yasa suka hanzarta isa wurin

Osun - 'Yan agajin kungiyar tsaron yanki Amotekun na jihar Osun sun yi ram da wani mutumi mai shekaru 47 da ya kutsa cikin majami'ar Cheribum ta Seraphim cikin anguwar Ogo-Oluwa a Osogbo.

Fashi da makami
An Damke Mutumin da Yayi Fashi a Coci, Dauke da Kayan da ya Kwasa. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Bashir Adewimbi, birgediya-janar mai ritaya kuma kwamandan Amotekun na jihar, ya ce wanda ake zargin ya kutsa cikin majami'ar da misalin karfe 4:00 na safiyar Juma'a.

Kara karanta wannan

An Kama Dan Sanda Da Ya Bindige Dattijuwa Yar Shekara 80 Har Lahira A Adamawa

Ya shaida wa manema labarai a ranar Asabar yadda aka kama wanda ake zargin bayan wani mazaunin yankin ya sanar wa 'yan agajin, jaridar TheCable ta rahoto.

" 'Yan agajinmu sun samu kiran gaggawa daga mazauna Ogo-Oluwa cewa an balle wata majami'a, ana bukatar 'yan agajinmu su hanzarta kama wanda ake zargin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Jami'anmu sun hanzarta daukar mataki, inda suka yi nasarar cafke wanda ake zargin yayin kokarin yin awon gaba da kayayyakin da ya sata a wurin."

- A cewarsa.

Mr Adewinmbi ya ce an kama mutumin da ake zargi da na'urar daukar murya, na'urar kara karfin murya, ganguna da sauran kayayyaki, Premium Times ta rahoto.

Kwamandan ya ce an mika wanda ake zargin hannun 'yan sanda don cigaba da bincike.

Ya bukaci mazauna yankin da su cigaba da samar da bayanan da zasu taimaka wajen cafke hatsabibai a jihar.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kai Hari Sansanin Horaswa Ta Hukumar INEC

Ya kara da rokon mazaunan da su yawaita fallasa duk wanda suke zargi da mumanan ayyuka yankin.

Matar aure ta je kotu tsinka igiyar aure kan rashin bata hakkinta

A wani labari na daban, wata matar aure ta maka mijinta a gaban kotu bayan tace baya bata hakkinta na aure.

Ta sanar da cewa yana dukanta, naushi da cin zarafi duk lokacin da ya so kuma baya kula da hakkokinsa na ciyar da ita da 'dansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel