Matar Aure ta Maka Miji a Kotu Kan Kaurace Mata Wurin Kwanciyar Aure
- Wata mata aure 'yar kasuwa, Ojoma Noel ta dira gaban kotu a Nyanya da ke Abuja, inda ta bukaci a raba aurenta da mijinta Thomas bisa tauye ma ta hakkin aure
- Matar mai 'da daya ta bayyana yadda ta ke fuskantar wulakanci da cin zarafi daga mijinta, wadanda suka hada da mare-mare, naushi, da kulle
- Ta bukaci kotu ta bata damar kula da 'dansu tare da tilasta shi ya dinga biyanta N50,000 na kula da shi duk karshen wata
Abuja - Wata mata 'yar kasuwa, Mrs Ojoma Noel, a ranar Alhamis ta maka mijinta, Thomas Noel wata kotu a Nyanya da ke Abuja bisa kin sauke ma ta hakkin aure da cin zarafinta.
Mrs Noel, wacce ta roki kotu da ta raba aurensu, ta ce, yanzu mijin nata ya daina kula da ita da 'dan su daya, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda ta shaida wa kotu:
"Mijina ya ki sauke min hakkina; ba ya damuwa da sanin yadda nake ji ko abubuwan da nake bukata ta kowanne bangare.
"Na fuskanci cin zarafi da wulakanci ba adadi daga Thomas, duk da naushi, mare-mare, kulle a gida da sauransu."
Ta roki kotu da ta bata kulawar 'dansu daya gami da umartar mijinta da ya dinga bata N50,000 a matsayin kudin kula da 'dan duk wata.
Mijin ya ki amsa duk zargin da ake masa, inda ya bukaci kotu da ta sulhuntasu.
Alkali mai shari'a, Doocivir Yawe ya dage sauraron karar zuwa 16 ga watan Fabrairu.
Ku raba mu, kada bakin cikin matata yayi ajalina, Magidanci a Abuja
A wani labari na daban, wani magidanci ya maka matarsa ta aure a gaban wata kotu a Abuja inda yake bukatar a raba aurensu na tsawon shekaru.
Magidancin ya bayyana yadda matarsa ke ficewa aiki ta barsa kuma ta ke masa boye-boye tare da kumbuya-kumbuya.
Yace a tsawon shekaru da suka yi tare kuma tana aikin gwamnati, bai taba sanin yawan albashinta ba.
Magidancin yace a hanzarta raba aurensu saboda bakin cikin da ta ke kunsa masa zai iya yin ajalinsa gaba daya, lamarin da alkalin yace a gwada yin sulhu.
Asali: Legit.ng