'Yan Kauye Sun Kama Rakumi Sun Sheke Bayan da Ya Kutsure Kan Mai Shi a India
- Wani rakumi a garin Rajasthan na kasar India ya taune kan mai shi, ahali da mutanen kauye sun taru sun kashe rakumin
- An ce Sohanram Nayak, mai ragumin yana kokarin kamo shi sadda ya kubuce daga inda ya daure shi ya bi wani ragumin a kauyen Panchu na Rajasthan.
- Daga nan ne ragumin ya daga mai shi ta wuya, ya buga da kasa kana ya taune kansa ya cinye
An lakadawa wani rakumi dukan mutuwa a wani kauye a jihar Rajasthan a kasar India bayan kashe mai shi.
Mai rakumin, Sohanram Nayak ya yi kokarin kama dabban ne a lokacin da ya kubuce, amma ya daga shi ta wuya, ya buga da kasa, kamar yadda The Times of India ta ruwaito a ranar Laraba 9 ga watan Faburairu.

Kara karanta wannan
Kaico: Jinkirin 'alert' yasa ikitoci sun ki kula mata mai juna biyu, sun barta ta mutu a Kano
An ruwaito cewa, bayan daga mutumin ta wuya, rakumin ya kada da kasa, ya kuma taune kansa gaba daya.

Asali: Twitter
Wannan lamari ya tunzura mutanen kauye da ahalin mamacin, don haka suka yanke shawarin daukar mataki a kai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Matakin da aka dauka
A cewar rahoto, mutanen kauye da ahalin nasa sun taru tare da rike sanduna bayan daure rakumin, suka lakada masa duka har ya mutu.
A cewarsu, sun yi hakan ne domin kubutar da kansu da kuma kare faruwar irin wannan lamari ga wani a nan gaba.
Bidiyon yadda aka yiwa rakumi dukan mutuwa
A bidiyon da ya bazu a kafar sada zumunta, an ga mutane rike da sanduna suna yiwa rakumin rubdugu.
Sun yi hakan ne bayan samun nasarar daure rakumin a jikin bishiya, kuma sun yi nasarar kashe shi
To abin tambaya, meye doka ta tanada ga dabbobin da ke kashe mutane? Kana meye doka ta tanada ga mutanen da suka kashe dabba ba don ci ko hadaya ba?
Ga dai bidiyon anan ku sha kallo.
Matar da ke tafiya da zakuna ta ba da mamaki
An ce kowa da kiwon da ya karbe shi, wani rakumi ya hallaka shi, wata kuma zakuna ne abokan tafiyarta.
A wani bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta, an ga lokacin da wata mata ke tafiyar kasaita da wasu manyan zakuna tana rike da sanda.
Mutane a kafar sada zumunta sun rasa ta cewa, sun bayyana martaninsu game da kaduwa da ganin wannan lamarin.
Asali: Legit.ng