Yan Daba Sun Kashe Wani Yayin Da Suka Kai Hari Mugun Kasuwar Bauchi

Yan Daba Sun Kashe Wani Yayin Da Suka Kai Hari Mugun Kasuwar Bauchi

  • Wasu matasa da ake zargin yan daba ne sun tafka ta'addi a kasuwar Wunti da ke jihar Bauchi
  • Maharan dauke da adduna, sanduna, wukake da sauran muggan makamai sun kutsa kasuwar ne ranar Asabar bayan kamfen din PDP a ranar Asabar
  • Yan bijilante sun bi sahun maharan sun yi nasarar kama guda 25 cikinsu kuma za a mika su ga yan sanda

Jihar Bauchi - Wasu da ake zargin yan daba ne sun kai hari kasuwar Wunti da ke jihar Bauchi inda suka kashe mutum daya tare da raunata wasu da dama, rahoton The Punch.

Babban mashawarci na musamman ga gwamnan jihar Bauchi, Umar Aliyu Shayi, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin magana da yan jarida.

Jihar Bauchi
Yan Daba Sun Kashe Wani Yayin Da Suka Kai Hari Kasuwar Bauchi. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Karancin Naira: El-Rufai ya fadi abu 1 da gwamnoni 36 suka roki Buhari ya yiwa talakawa

Ya ce yan daba wadanda shekarunsu ya kama daga 18 zuwa 25, dauke da adduna da sanduna da wukake da wasu makamai da suka kai wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba hari.

Ya ce:

"An sanar da ni abin da ke faruwa kuma nan take ni da mutane na muka tare su a shataletalen Wunti, yawansu ya dara 200 suna rike da muggan makamai amma mun iya kama 25 cikinsu kamar yadda ka gani a nan.
"An kama wadannan bata garin ne yayin da suke kwacewa mutane wayoyinsu, kudi da sauran abubuwa masu muhimmanci a kasuwar Wunti.
"Sun shiga filin wasa, inda aka yi taron dan takarar shugaban kasa na PDP, suka kaiwa mutane hari suka kwace wayoyinsu da jakuna yayin da suka raunata wasu da makamansu."

Shayi, wanda kuma shine kwamandan hukumar bijilante da tallafawa matasa ya ce:

"Bayan taron yakin neman zaben, sun kutsa kasuwar Wunti da ke kusa da wurin da nufin yi wa mutane da yan kasuwar fashi."

Kara karanta wannan

Canjin Kudi: Makiya Dimokradiyya Ne Ke Son Kawo Rudani A Najeriya, In Ji Tinubu

Ya kara da cewa yan bijilante na jihar za su hada gwiwa tare da jami'an tsaro domin rage laifuka a jihar kuma za a mika wadanda aka kama hannun yan sanda don hukunta su.

Mahara sun kutsa tashar jirgin kasa sunyi awon gaba da bayin Allah

A gefe guda wasu mahara sun kutsa tashar jirgin kasa da ke karamar hukumar Igueben a jihar Edo.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wadanda aka sace din suna shirin shiga jirgi ne domin tafiya birnin Warri yayin da aka kai musu harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel