Mun Roki Buhari da Ya Bari a Ci Gaba da Amfani da Sabbin Kudi da Tsoffi a Hade

Mun Roki Buhari da Ya Bari a Ci Gaba da Amfani da Sabbin Kudi da Tsoffi a Hade

  • Gwamnonin Najeriya 36 sun tsoma baki game da sauya fasalin Naira da rikicin da ke tattare dashi na kwanan nan
  • Yayin ganawa da Buhari a Abuja ranar Talata 7 ga watan Faburairu, gwamnonin sun ba da shawarin a ci gaba da amfani da sabbi da tsoffin kudi a hade
  • Wannan shawari da gwamnonin suka bayar na fitowa ne daga bakin El-Rufai a wani bidiyon da Joe Igbokwe ya yada

An yi shawari mai kyau tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohi 36 na Najeriya, sun fadi abin da suke so a yi game da batun sauyin kudi.

A wani bidiyon da Joe Igbokwe ya yada a ranar Laraba 8 ga watan Faburairu, an ji gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa na bayyana abin da gwamnonin kasar suka roki Buhari ya yi game da sabbin kudi da tsoffi.

Kara karanta wannan

A ina kika samo: Kowa girgiza, wata mata ta samo damin kudi, tana siyar da N50k a farashin N60k

A cewarsa, sun roki Buhari da ya bari a ci gaba da amfani da tsoffin kudade tare da sabbin a hade yayin da za ci gaba da musayarsu a hankali har su shiga hannun CBN.

El-Rufai ya fadi abin da gwamnoni suka roki Buhari ya yiwa talakawa
Mun Roki Buhari da Ya Bari a Ci Gaba da Amfani da Sabbin Kudi da Tsoffi a Hade | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Ba a Najeriya aka taba sauya kudi ba, El-Rufai ya ba da misali

Ya kuma bayyana cewa, ba wannan ne karon farko da wata kasa a duniya ta kawo batun sauyin fasalin kudi ba, kasashe da yawa sun yi hakan a baya, ciki har da Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce ya kamata a samu wadatuwar sabbin kudi, yayin da tsoffin kudin za su bace a hankali daga hannun jama’ar kasar.

Gwamnan ya ba da misali da kasar Saudiyya da Burtaniya, inda yace an yi sauyin kudi kuma tsoffin sun bace an ci gaba da amfani da tsoffi ba tare da wata matsala ba.

Kara karanta wannan

"Nima Ina Ji A Jiki Na", Minista Mai Karfi A Gwamnatin Buhari Ya Ce Shi Kansa Ba Shi Da Sabbin Takardun Naira

Zabe zai kankama cikin tsanaki

A wani labarin, kunji yadda gwamnan CBN ya gana da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta don tattauna alakar zabe da sauyin kudi da kasar nan ta taso dashi.

A ganawarsu, gwamnan CBN ya ce, babban bankin zai samar da duk abin da ake bukata na hadin kai don tabbatar da an yi zaben 2023 cikin tsanaki ba tare da matsala ba.

Hakazalika, ya ce duk adadin kudaden da INEC ke bukata don yin jigilar zabe, babban bankin zai samar dasu ba tare da bata lokaci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.