Karancin Naira da Tsadar Mai: Rikici Ya Barke a Abeokuta Yayinda Matasa Suke Gudanar da Zanga-Zangar

Karancin Naira da Tsadar Mai: Rikici Ya Barke a Abeokuta Yayinda Matasa Suke Gudanar da Zanga-Zangar

  • Matasa sun fara bayyana bacin ransu bisa karancin tsabar kudi a cikin al'ummar Najeriya
  • Zanga-zanga ya barke a jihohi daban-daban musamman daga kudancin Najeriya
  • An kona bankuna, tayoyi kuma an yi rashin rayuka da dama cikin wannan hayaniya

Wani zanga-zanga ya barke a birnin garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun yai Talata inda matasa suka bazama cikin gari bisa karancin Naira da halin da ya jefa rayuwar mutane.

Fusatattun matasan sun kai farmaki bankin First Bank dake Sapon inda suka yi kokarin banka mata wuta.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da lamarin ya bayyana cewa suna lura da lamarin gudun kada ta sauya zani.

SP Abimbola ya bayyana cewa suna zargin akwai matasa masu niyyar tayar da tarzoma.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa jami'an yan sandan na harbin masu zanga-zangar haka kawai.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wasu Tsageru Sun Yanka Jagoran APC Har Lahira Bayan Tinubu Ya Ci Zabe

Yanzu haka matasa sun bazama cikin garin suna kona tayoyi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Karancin Mai Da Kudi: Rikici Ya Barke a Wata Jihar Kudu, An Kashe Mutum Daya

Zanga-zanga kan karancin man fetur da Naira ya yi sanadiyar rasa ran mutum daya a Ibadan, babban jihar Oyo.

An kashe mutumin wanda ya kasance mamba a kungiyar yan sa-kai a ranar Asabar, 4 ga watan Fabrairu, a yankin Apata da ke Ibadan yayin arangama tsakanin jami'an tsaro da wasu da ake zaton yan daba ne.

Adewale Osifeso, kakakin yan sandan jihar, ya bayyana cewa wasu yan daba sun farmaki jami'an tsaro yayin da suke fatrol a wajajen mararrabar kasuwar Apata, jaridar The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel