Borno: Rayukan Mayakan ISWAP da Boko Haram Sun Salwanta a Sabuwar Arangama

Borno: Rayukan Mayakan ISWAP da Boko Haram Sun Salwanta a Sabuwar Arangama

  • Arangamar tsakanin kungiyoyin ta'addanci na Boko Haram da ISWAP yayi ajalin mayakan masu tarin yawa
  • An gano cewa, an yi mummunar arangamar ne a tsakanin yankunan Kuwa Nguori da kauyen Ngoldiri dake kusa da Timbuktu
  • Bayanai da aka tattaro sun sanar da cewa, Boko Haram tana hada gagarumar kungiyar kai harin daukar fansa karkashin wani Alhaji Ali Hajja Fusam

Borno - 'Yan ta'addan ISWAP da Boko Haram sun yi wata arangama a yankin Kuwa Nguro da kauyen Ngoldiri a kusa da Timbuktu da ke Damboa a jihar Borno.

Taswirar Borno
Borno: Rayukan Mayakan ISWAP da Boko Haram Sun Salwanta a Sabuwar Arangama. Hoto daga theacable.ng
Asali: UGC

Wannan ya faru ne kasa da sa'o'i 24 bayan wani fadan adawa ya barke a yankin Tumbun Gini yayin da ISWAP suka farmaki mayakan Boko Haram da ke zuwa yankin.

An tattaro yadda wannan fadan ya faru ranar 7 ga watan Fabrairu a Timbuktu wanda aka kwashe sa'o'i 3 ana yi, hakan yayi ajalin mayakan masu yawa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Tsageru Suka Bindige Limami, Suka Sace Mutum 14 a Jihar Kaduna

Shahararren wallafar da ta kware wurin yaki da ta'addanci a yankin Chadi, Zagazola Makama, ta bayyana cewa, mayakan da yawa sun samu rauni yayin da aka kwace wasu makamai da babura daga tsagin Boko Haram.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Akwai yuwuwar cigaba yaki tsakanin kungiyoyin ta'addancin biyi a Sambisa, Marte da Abadam.

Kungiyar Boko Haram a daya bangaren suna shirya manyan mayakansu a dajin Sambisa da tsaunin Mandara domin fito na fito da mayakan ta'addanci na ISWAP.

Domin tabbatar da karfin kungiyar, Boko Haram ta nada wani Alhaji Ali Hajja Fusam, 'dan asalin Bama matsayin shugaban 'yan ta'addan Gaizuwa, wani sansani da dakarun sojin Najeriya suka lalata ba sau daya ba ko sau biyu.

Cigaba arangama tsakanin kungiyoyin JAS da ISWAP alamu na nuna ba zata kare ba saboda dukkan bangarorin biyu suna neman yadda zasu hada kai da rundunar sojin Najeriya da MNJTF amma hakan yaa ci tura.

Kara karanta wannan

Karancin Mai Da Kudi: An Yi Kare Jini Biri Jini Yayin Zanga-zanga a Wata Jahar Najeriya, An Kashe Mutum Daya

Yayin da wannan cigaban ke zama abun alheri ga dakarun sojin Operation Hadin Kai, akwai yuwuwar irin wannan arangamar ta zama karshen kungiyoyin ta'addancin.

EFCC ta kama manajan bankin a Abuja kan boye N29 miliyan

A wani labari na daban, hukumar EFCC ta damke wani manajan bankin 'yan kasuwa a Abuja bayan an kama N29 miliyan a lalitar bankin.

Manajan ya hana jama'a a ATM tare da badawa a kanta duk da kuwa layin da aka dinga zabgawa a ranar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel