Yan Bindiga Sun Kashe Limami, Sun Yi Garkuwa Da Mutum 14 a Sabon Harin Kaduna

Yan Bindiga Sun Kashe Limami, Sun Yi Garkuwa Da Mutum 14 a Sabon Harin Kaduna

  • Yan bindiga sun halaka babban limamin masallacin Juma'a da ke Rugan Ardo, Isyaka Adamu, a yankin Kagarko da ke jihar Kaduna
  • Tsagerun sun kuma kashe dan shugaban Fulanin yankin, Alhaji Husaini Ardo, sannan suka yi awon gaba da mutum 14
  • Zuwa yanzu ba a samu jin ta bakin rundunar yan sandan jihar Kaduna ba a kan wannan mummunan al'amari

Kaduna - Tsagerun yan bindiga sun bindige babban limamin masallacin Juma'a da ke Rugan Ardo, Isyaka Adamu da dan shugaban Fulani sannan suka sace wasu 14 a karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, Daily Trust ta rahoto.

Yadda abun ya faru, mazaunin yankin

Wani mazaunin yankin da ya tabbatar da kisan da sace mutanen ta wayar tarho mai suna, Shehu Ibrahim, ya ce yan bindigar sun farmaki garin Janjala sannan suka yi awon gaba da mutum takwas.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Dauke da 'Bama-Bamai' Sun Sake Kai Kazamin Hari Kan Ɗan Takarar PDP

Jihar Kaduna
Yan Bindiga Sun Kashe Babban Limami, Sun Yi Garkuwa Da Mutum 14 a Sabon Harin Kaduna Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Bayan nan sun isa Rugan Ardo, yan kilomita kadan da Janjala inda suka sace mutum shida bayan sun kashe daya daga cikin yaran shugaban yankin, Alhaji Husaini Ardo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa an sace takwas daga cikin mutanen 11 a Disambar 2022 a Janjala kuma har yanzu suna nan a hannun wadanda suka yi garkuwa da su bayan sun sako uku daga cikinsu a makon jiya.

Ya kara da cewa:

"Har yanzu babu jami'in tsaro da ya ziyarci kauyen duk da cewar an sanar da yan sanda lokacin da harin ke gudana."

Martanin yan sanda

Zuwa yanzu babu wani martani ko cikakken bayani daga rundunar yan sandan jihar Kaduna kan wannan al'amari.

Yan bindiga sun ki karbar kudin fansa da tsoffin naira

A halin da ake ciki, an tattaro a baya cewa wasu yan ta'adda sun ki amsar tsakardun tsoffin kudi naira miliyan 5.3 da aka kai masu a matsayin kudin fansa, cewa wa'adin daina amfani da su ya kusa cika.

Kara karanta wannan

Karancin Mai Da Kudi: An Yi Kare Jini Biri Jini Yayin Zanga-zanga a Wata Jahar Najeriya, An Kashe Mutum Daya

Sahara Reporters ta rahoto cewa shugaban yan bindigar, wanda suka farmaki garuruwan Azara, Janjala da Kadara a jihar Kaduna a ranar 12 ga watan Disambar 2022 tare da sace mutum 37 sun bukaci yan uwan wadanda suka sace su mayar da tsoffin kudin da suka kai masu kudin fansar.

Maimakon haka, ya bukaci a kawo kayan abinci, magunguna da lemun kwalba kafin ya saki wasu masu jego biyu da maza uku daga cikin mutane 11 da ya sace a garin Azara da ke karamar hukumar Kachia.

An yi wa dan gudun hijira yankar rago a jihar Borno

A wani labari na daban, wani magidanci ya yi wa wani dan gudun hijira a jihar Borno yankar rago saboda ana zarginsa da maita, kuma cewa shine ya yi sanadiyar mutuwar mai dakin makashin nasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel