EFCC Tayi Ram da Manajan Bankin 'Yan Kasuwa a Abuja kan Boye Sabbin Kudi

EFCC Tayi Ram da Manajan Bankin 'Yan Kasuwa a Abuja kan Boye Sabbin Kudi

  • Hukumar EFCC ta damke manajan babban bankin 'yan kasuwa a kwaryar birnin Abuja bayan ta kama N29 miliyan a ma'adanar kudinsu
  • Kafin jami'an su tafi da shi don tuhuma, sun umarci a zuba kudin a ATM tare da fara biyan kwastomomin ta kanta
  • EFCC tayi kira ga 'yan Najeriya da su nemi daukinta matukar suka je bankunan aka hana kudi kuma suka zargi akwai su an boye ne

FCT, Abuja - Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta kama manajan ayyuka na wani bankin 'yan kasuwa kan boye sabbin takardun naira a Abuja.

Hukumar EFCC
EFCC Tayi Ram da Manajan Bankin 'Yan Kasuwa a Abuja kan Boye Sabbin Kudi. Hoto daga Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Manajan ayyukan babban bankin 'yan kasuwa da ke kwaryar birnin Abuja a yau, 6 ga Fabrairun 2023, ya shiga hannun jami'an EFCC kan kin zuba kudi a ATM din bankin duk da N29 miliyan da aka samu na sabbin kudin a ma'adanar kudin bankin.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda ICPC Ta Farmaki Banki, Ta Bankado Sabbin Naira Boye a Durowa

Kamar yadda EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook, kafin a yi awon gaba da shi don tuhuma, jami'an sun umarci a zuba kudin a ATM kuma a fara biya ta kanta domin rage radadi ga kwastomomin da suka kwashe awoyi a layi.

Wannan bankadowar ya bayyana zagon kasa ga dokokin kudi na gwamnati wanda wasu bankunan ke yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukumar EFCC za ta cigaba da zagaye tare da sa ido da kuma kai ziyarar ba-zata bankuna a fadin kasar nan domin duba ma'adanar kudinsu tare da tantancewa ko da gangan suke kin zuba sabbin kudin.

Sama da rassa biyar na bankuna a yau jami'an EFCC suka mamaye a Abuja. An yi irin hakan a wasu sassan kasar nan.

Kamar yadda hukumar EFCC ta tabbatar, jami'anta za su cigaba da irin haka har sai komau ya dawo daidai a kasar.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: An kama manajan bankin da ke boye sabbin kudi yana hana 'yan Najeriya

Hukumar yaki da rashawan tayi kira ga 'yan Najeriya da ke wahalar samun kudi a kowanne banki kuma suke zargin akwai zagon kasa da su tuntubi hukumar domin kawo musu daukin gaggawa.

'Yan daba sun farmaki matar Gwamna, ta sha da kyar

A wani labari na daban, 'yan daba a yankin Mubi sun kai wa matar Gwamnan Adamawa, Lami Ahmadu Fintiri, farmaki.

Sun dinga jifan tawagarta da sanda tare da duwatsu inda ta sha da kyar amma suka illata mutum daya a tawagar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel