Miliyan 1 Nake Biya Duk Shekara: Matashi Ya Baje Kolin Hadadden Gidan Da Yake Haya a Bidiyo

Miliyan 1 Nake Biya Duk Shekara: Matashi Ya Baje Kolin Hadadden Gidan Da Yake Haya a Bidiyo

  • Wani matashi dan Najeriya da ke zama a Lagas ya baje kolin katafaren gidan da yake biyan haya naira miliyan 1 duk shekara
  • Mutumin wanda ya kewaya don nuna lungu da sako na gidan mai dakuna uku ya ba mutane mamaki duba da yadda ya kawata gidan
  • Daga cikin wadanda suka yi martani ga bidiyon gidan akwai masu amfani da TikTok da suka ce farashinsa ya fi haka a wasu yankunan

Wani hazikin dan Najeriya mai suna @walesmorqan, wanda ke yin bidiyoyi masu kayatarwa a TikTok ya tambayi wani mazaunin Lagas nawa yake biya kudin hayar gidansa duk shekara.

A lokacin da mutumin ya fada masa naira miliyan 1.180, matashin ya nemi ya sakaya da shi cikin gidan don mutane su ganewa idanunsu.

Matashi da gida
Miliyan 1 Nake Biya Duk Shekara: Matashi Ya Baje Kolin Hadadden Gidan Da Yake Haya a Bidiyo Hoto: @walesmorqan
Asali: UGC

Hadadden gidan haya a Lagas

Gidan wanda ke yankin Awoyaya na jihar yana dauke da dakuna uku da wani dakin waka. Gidan mutumin ya sha gyara sosai da kayan alatu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani bangare na gidan na dauke da furannin roba hange a saman silin. Yadda aka kawata cikin gidan ya baiwa @walesmorqan sha'awa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Scarlett ya ce:

"A lokacin da na ga furannin nan take na san cewa yana da mace wacce ta tsara gidan."

Chisom Samuel ta ce:

"Gidana a Agege N60k nake biya shekara..amma na yarda zan kan matsayinsu."

clair Becky 456 ta ce:

"Wannan gidan ya hadu matuka."

37threads_ng ya ce:

"Ina a Lagas??? Ina bukatar irin wannan gidan."

Gabby.042ya ce:

"Lol ya kamata wannan ya fi 1.8m koda dai ya danganta da inda gidan yake."

Damii ta ce:

"Tsaya, 1.1M??? Wannan ya fi 2M a Abuja."

Kemisola ta ce:

"Gayen nan ya karya mun zuciyata ka yi aure."

Kyakkyawar matashiya mai dirarriyar sura ta dauka hankali a intanet

A wani labarin, mun ji cewa jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da bidiyon wata kyakkyawar mata yar arewa wacce ke dauke da kyakkyawar sura a wajen wani taron biki.

Matar ta fito ta koro jawabi a wajen taron inda mijinta ya cika da alfahari da ita tare da yi mata yayyafin kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel