Yan Sanda Sun Gurfanar Da Magidanci Kan Ya Auri Mata Ta Biyu

Yan Sanda Sun Gurfanar Da Magidanci Kan Ya Auri Mata Ta Biyu

  • Edmund Uzoma ya gurfana a gaban kotu majistare da ke Yaba, jihar Lagas kan wasu tuhume-tuhume da ake masa
  • Yan sandan Lagas sun gurfanar da magidancin a kan zargin kara aure bayan kuma yana da mata tare da bayar da bayanan karya wajen daurin auren
  • Wanda ake karar bai amsa lafinsa ba inda kotu ta bayar da belinsa kan kudi naira miliyan daya

Lagos - Rundunar yan sanda ta gurfanar da wani mutum mai suna Edmund Uzoma, a gaban kotun Majistare da ke Yaba, jihar Lagas a ranar Laraba, 1 ga watan Fabrairu, kan zargin kara aure.

An gurfanar da Uzoma gaban mai shari'a Adeola Olatunbosun kan tuhume-tuhume guda uku na yin aure cikin aure da bayar da bayanan karya wajen cike takardar aure.

Yan sanda
Yan Sanda Sun Gurfanar Da Magidanci Kan Ya Auri Mata Ta Biyu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Dan sanda mai shigar da kara, Idowu Osungbure, ya fada ma kotu cewa Uzoma wanda ke da mata ya sake kulla wani auren da Sophia Yongxian, a wajen rijistan aure, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Masu Son Gaje Buhari Abin Dariya Ne, Gwamnan Arewa Ya Tabo 'Yan Takarar Shugaban Kasa

Angon ya ce shi gwauro ne da aka zo daura masa aure na biyu

Ya kuma bayyana cewa wanda ake karar ya kuma bayar da bayanan karya cewa shi din gwauro ne yayin da yake nan da matar aure a gida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Osugbure ya yi zargin cewa Uzoma ya aikata laifin ne a 2019, yana mai cewa hukuncin laifukan na nan a karkashin sassa na 411 da 115 na dokar aikata laifi na jihar Lagas da kuma sashi na 370 na aikata laifuka Act Cap. C. 38 na dokar tarayya, 2004.

Wani bangare na tuhumar na cewa:

"Cewa kai, Edmund Uzoma, na unguwar Lekki Road 15, Golden Gate Apartment, Lagos, wani lokaci a 2019 a yankin Lagas, ka aikata laifi na aure cikin aure da kuma bayanan karya."

Kotu ba wanda ake kara beli

Kara karanta wannan

Assha: Dan takarar majalisa a jam'iyyar su Kwankwaso a Arewa ya sace N681m daga asusun banki

Wanda ake karar bai amsa tuhume-tuhumen da ake masa ba.

Mai shari'a Olatunbosun ta bashi beli ta hanyar biyan naira miliyan daya da mutane biyu da zasu tsaya masa.

Ta ce dole daya daga cikin wadanda za su tsaya masa ya kasance yana da kadara ta fili a Lagas.

Ta dage sauraron shari'ar har zuwa ranar 15 ga watan Maris din 2023, rahoton Daily Post.

Amarya ta fasa aurenta ana gobe biki bayan ta gano wani sirri na angonta

A wani labari na daban, wata amarya ta soke aurenta a ranar jajiberin bikinta bayan ta gano cewa bashi ya yi wa mai shirin zama angonta katutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel