An Kama Wani Dan Najeriya a India Bisa Zargin Aikata Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi

An Kama Wani Dan Najeriya a India Bisa Zargin Aikata Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi

  • 'Yan sandan kasar India sun kama wani dan Najeriya da ke safarar kwayoyi a yankuna Kerala, Karnataka
  • An kama kama mutumin ne dauke da miyagun kwayoyi, za a gurfanar dashi a gaban kuliya manta sabo
  • Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana matakin da aka dauka a kansa ba, amma an ce ya jima yana harkar kwaya a kasar

Bengaluru, India - ‘Yan sandan kasar India sun kama wani dan Najeriya mai suna Charles Diffodile bisa laifin safarar haramtattun miyagun kwayoyi daga Bengaluru zuwa Kerala a kasar ta India.

An kama mutumin ne dauke da kilogiram 55 na Methylenedioxymethamphetamine, kamar yadda rahoton Punch ya bayyana.

Binciken ‘yan sanda daga baya ya bayyana cewa, mutumin ya kasance babban dan harkallar miyagun kwayoyi a yankuna daban-daban na Kerala.

An kama dan Najeriya a India
An Kama Wani Dan Najeriya a India Bisa Zargin Aikata Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Dama ya kasance dan harkallar kwayoyi, ba wannan ne karon farko ba

Kara karanta wannan

Jami’an NDLEA Sun Kama Mata Mai Juna Biyu Da Miyagun Kwayoyi A Cikin Rediyo

An kuma bayyana cewa, Diffodile ya kasance cikin wani zargi na safarar miyagun kwayoyi kafin daga bisani aka sake yin nasarar kama shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar jaridar Times of India, ‘yan sanda sun ce:

“Yana harkallar miyagun kwayoyi a cikin yankuna masu yawa na Kerala. ‘Yan sanda na bincike ne kan wani laifin miyagun kwayoyi wanda ya kai ga kama Charles daga Bengaluru, Karnakata. Dama an taba ba da belinsa a baya kan zargin harkallar kwaya.”

A bidiyon da jaridar ta yada, an ga dan Najeriyan daure da ankwa a tsakanin ‘yan sanda masu yawa a lokacin da shugaban ‘yans sandan ke magana da manema labarai.

Ba wannan ne karon farko da ake kama 'yan Najeriya a wasu kasashe suna harkallar migaun kwayoyi ba, an sha yin hakan a baya.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Babu laifin Buhari, Peter Obi ya ce 'yan Najeriya su hankalta, su yiwa Buhari uzuri

An kma dan Najeriya da tarin kudade a kasar Burtaniya

A wani labarin, an kama wani dan Najeriya a kasar Burtaniya dauke da manyan kudaden kasar waje makare a cikin wani akwatin da ke dakinsa.

'Yan sandan kasar ne suka yi dafifi domin bincikar dakin tare da gano yadda aka kushe wasu kudade da ake zargin an samo su ne ta haramtattun hanyoyi da ba a sani ba.

A lokacin da ake binciken, an nemi matashin da ya ba da hadin kai domin yin bincike cikin sauki don gano tushen komai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel