Aisha Buhari Na Daya Daga Cikin Masu Hana Ruwa Gudu a Fadar Shugaban Kasa, Inji Naja’atu Mohammed
- Naja’atu Muhammad ta tono batutuwan da suka shafi zurku da kitse-kitse da ke faruwa a fadar shugaban kasan Najeriya
- Ta ce, Aisha Buhari na daya daga cikin masu kawo tsaiko ga abin da ke faruwa a fadar Buhari tun bayan rasuwar Abba Kyari
- Maganganu masu daukar hankali na ci gaba da fitowa daga bakin Naja’atu tun bayan da ta fice daga jam’iyyar APC mai mulki
Najeriya - Tsohuwar daraktar gangamin kamfen an APC, Hajiya Naja’atu Mohammed ta tona wani asiri, ta ce uwar gidan Buhari na daga cikin wadanda ke hana ruwa gudu kuma masu kits-kitse a fadar shugaban kasa, Punch ta ruwaito.
Naja’atu ta tono wannan batun ne tare da cewa, Aisha Buhari ta jima tana shirya makarkashiya a Aso Rock tun bayan hawan Buhari mulki.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya ce akwai wasu masu hana ruwa gudu a da ke cin dunduniyar Tinubu kan zabe mai zuwa.
A cewar El-Rufai, akwai wasu mutane da yawa a fadar shugaban kasa da ke yin duk mai yiwuwa don ganin Tinubu bai ci zaben 2023 ba, Daily Post ra ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aisha Buhari ne mai hana ruwa gudu
Da take magana a ranar Litinin da safe a shirin Morning Show na Arise Tv, Naja’atu ta fadi magana mai kama da na El-Rufai, inda ta bayyana daya daga cikin masu hana ruwa gudu.
Da take bayani, ta ce:
“A da marigayi Abba Kyari ne shugaban masu kitse-kitse, Allah ya gafarta masa, abin da yasa Aisha Buhari a baya take sukarsu, kawai saboda ba ta cikinsu ne.
“Amma yanzu ta yi nasarar korar Mamman Daura daga Villa. Da kanta ta kore su.
“Idan za ka tuna batun harbe-harbe a cikin Villa, harbi a cikin Villa, waye ya yi hakan?
“Gungun masu kitse-kitse na Aisha Buhari ya hada ne da ‘ya’yanta da ‘yan uwanta maza, ita ke yanke shawarin nada tsohon DG na NISER.
“Ita ta yi shawarin kawo wani, wanda dan uwanta ne, uwa daya, uba daya a fannin kamfanin buga kudi.
“A wasu lokutan ma, takan umarci shugabannin ma’aikatu, don haka waye ita? Shin ba ta cikin masu kitse-kitse?”
A baya ta ce, idan aka zabi Tinubu daidai yake da an ba matarsa mulkin kasar, domin ba zai iya yin komai ba.
Asali: Legit.ng