Sabbin Takardun Naira: Wadanda Suka Kulle Muku Kudi Za Su Bude Su, In Ji Tinubu

Sabbin Takardun Naira: Wadanda Suka Kulle Muku Kudi Za Su Bude Su, In Ji Tinubu

  • Tinubu ya bayyana cewa wahalar mai da kuma chanjin kudi shiri ne na kada shi zabe
  • Tinubu ya bayyana haka ne yayin da yake gangamin yaƙin neman zabe a Jihar Ekiti
  • Dan takarar na APC ya kuma roki jama'a su kwantar da hankali su kuma karbi katin zabe don dora shi a kan karaga

Jihar Ekiti - Dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya sake sukar kudirin chanjin kuɗi na babban bankin Najeriya, Daily Trust ta rahoto.

A satin da ya gabata lokacin da yake taron yaƙin neman zaɓe a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, Tinubu ya ce ƙarancin man fetur da kuma sabbabin dokokin babban banki (CBN) shiri ne na kada shi zaɓe.

Bola Tinubu
Sabbin Takardun Naira: Wadanda Suka Rufe Muku Kudi Za Su Bude, Tinubu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ankarar da Magoya-Baya a Kan Sirrin Jawo Wahalar Fetur da Karancin Nairori

Lafazin ya jawo cece kuce a sassan ƙasar nan.

Da yake kamfen a Ado Ekiti, babban birnin jihar, ranar Juma'a, Tinubu yace akwai wani shiri da wasu mutane ke yi don yin amfani da ƙarancin man fetur da kuma chanjin kudi don kawo rashin daidaito, wanda zai iya janyo ɗage zaɓen shugaban ƙasa ya kuma tilasta kafa gwamnatin riƙon ƙwarya.

Zaben 2023 lokacin Yarbawa ne, Tinubu ga mutanen Ekiti

Ya ce yanzu lokacin yarbawa ne na mulkar ƙasar nan, yana mai cewa ''wannan zaɓen naku ne. Zaɓe ne da za ku kafa kanku.''

Ya ce yanzu lokacin yarbawa ne na mulkar ƙasar nan, yana mai cewa ''wannan zaɓen naku ne. Zaɓe ne da za ku kafa kanku.''

''Wannan zaɓen ba saboda ni bane saboda ni ba neman abincin da zanci nake ba.
"Yoruba, Yoruba, lokaci waye? Ku kwantar da hankali, zaɓen nan naku ne. Zaku yi amfani dashi gina kanku. Suna son maida mu bayi. Mu ba bayi bane. Sun kulle kuɗi. Su kuma biko wajen zaɓen ku, suyi zaɓe su kuma kafa gwamnati. Na haɗa ku da Allah, wannan ba abin faɗa bane, kar kuyi faɗa da su. Wanda suka kulle muku kuɗi da sannu zasu buɗe. Suna yi don su fusata ku, don ku tada hargitsi.......... Duk ɓeran da ya ci guba shi ya kashe kansa."

Kara karanta wannan

Labari Mai Dadi: CBN Ya Gano Masu Ɓoye Miliyoyin Sabbin Kudi, Ya Fadi Abinda Ya Dace Mutane Su Yi

Ya kara da cewa, duk da kasancewar al'ummar Ekiti masu ilimi, amma matasa da yawa basu da aikin yi.

Tinubu ya yi kira ga mutanen da basu karɓi katin zaɓen su ba da su yi kokari su karba, ya kara da cewa "suna son riƙewa ne su hana ku. Kada ku ƙyale su."

Da yake jawabi, Gwamnan Jihar Ekiti, Mr Abiodun Oyebanji ya ce jam'iyyar bata buƙatar tallata Tinubu, ya ƙara da cewa, al'ummar jihar zasu saka masa da ƙuri'un su saboda ayyukan alherin sa.

"Bama buƙatar tallata Tinubu sosai. Mun yarda gaba ɗaya zamu zaɓe shi. Muna son saka masa kan ayyukan alherin sa ga Ekiti.
"Zamu koma gida kuma mu sanar da mutanen mu cewa lallai Tinubu za iya. Zamu fada musu kowa ya karbi katin zaben sa, duk wanda bashi da katin zabe ba abokin Asiwaju bane."

Ganduje: Yan arewa ba su da uzurin juya wa Tinubu baya

Kara karanta wannan

2023: Abinda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Faɗa Wa Atiku Yayin da Ya Je Kamfe Sakkwato

Dakta Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Kano ya ce al'ummar arewa ba su da wani uzurin rashin zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu a 2023.

Ganduje ya ce Tinubu ya taka rawar azo a gani wurin ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dare kan mulki, don haka lokaci ya yi da za a masa sakayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel