Sabbin Kudi: Gwamnatin Kaduna Ta Umurci Asibitoci Su Fara Karbar ‘Transfer’

Sabbin Kudi: Gwamnatin Kaduna Ta Umurci Asibitoci Su Fara Karbar ‘Transfer’

  • Gwamnatin Kaduna ta umurci asibitocin gwamnati da su dunga karbar 'transfer' daga wajen marasa lafiya
  • Hukumar KADIRS ta nemi asibitoci su koma karbar kudi ta asusun su kai tsaye don ragewa yan jihar radadin rashin takardun kudi da ake fama da shi
  • Tun bayan sauya kudi da saka wa'adin daina amfani da tsoffin kudi da CBN ya yi, yan Najeriya na fama da karancin kudi a fadin kasar

Kaduna - Hukumar tattara haraji ta jihar Kaduna (KADIRS) ta umurci dukkanin asibitocin gwamnati a jihar da su dunga yarda marasa lafiya na tura masu kudin asibiti ta asusun su kai tsaye wato 'Transfer'.

Hakan ya kasance ne saboda mawuyacin halin da yan Najeriya ke ciki a yanzu wajen samun tsoffi da sabbin kudi, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Fusatattun Matasa Yan Zanga-Zanga Sun Kai Hari Ofishin Gwamna

El-Rufai
Sabbin Kudi: Gwamnatin Kaduna Ta Umurci Asibitoci Su Fara Karbar ‘Transfer’ Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Gwamnatin Kaduna ta dade da haramta tsarin karbar kudi a hannu a asibitoci

Babban sakataren hukumar KADIRS, Dr. Ziad Abubakar, a wani taron manema labarai a ranar Asabar, 4 ga watan Fabrairu, ya bayar da tabbacin cewa suna aiki don samar da karin POS a dukkanin asibitocin gwamnai da ke fadin jihar don saukaka biyan haraji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dr. Abubakar wanda ke martani ga korafin cewa jami'an wasu asibitocin gwamnatin sun kafe sai dai a biya tsabar kudi yayin duba marasa lafiya, ya bayyana cewa tuni gwamnatin jihar Kaduna ta soke tsarin biyan kudi kan tebur.

Ya ce:

"Tun ma kafin a sauya kudin, gwamnatin jihar Kaduna ta soke sannan ta haramta karbar tsabar kudi, daidai da sashi na 51 na dokar kayyade haraji ta jihar Kaduna, 2020. Saboda haka, babu wata hujja da zai sa asibitocin gwamnati su ki yarda da karbar 'transfer' kai tsaye daga asusun banki."

Kara karanta wannan

Kuyi Hakuri Da Wahalar Karancin Naira Kamar Yadda Kuke Hakuri Da Shan Magani Idan Baku Da Lafiya: Ministar Kudi

Ya ce a wannan yanayi na rashin takardar kudi mafita da aka fi amfani da shi wajen hada-hadar kudi, siye da siyarwa shine tura kudi zuwa asusu kai tsaye.

Ya bayyana cewa duk da jinkirin da ake samu, 'tarnsfer' shine mafi guda daya na biyan kudade a asibitocin gwamnai, kamar yadda yake a dokar kayyade haraji da kuma halin da ake ciki a yanzu, rahoton TheCable.

Sauya takardun kuji ya jefa yan Najeriya a kunci, Fashola

A wani labarin kuma, ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola ya bayyana cewa sabon manufar CBN na sauya takardun kudi ya jefa al'ummar Najeriya a cikin kunci.

Fashola ya ce akwai bukatar babban bankin kasar ya sake bitar manufofinsa tare da janye su don saukakawa yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel