Kungiyar Lauyoyi Ta Yi Martani Mai Zafi Bayan ’Yan Bindiga Sun Kashe Alkali Yana Tsaka da Yanke Hukunci

Kungiyar Lauyoyi Ta Yi Martani Mai Zafi Bayan ’Yan Bindiga Sun Kashe Alkali Yana Tsaka da Yanke Hukunci

  • Kungiyar lauyoyi ta Najeriya ta yi Allah-wadai da kisan da aka yiwa wani alkali yana tsaka da yanke hukunci
  • A ranar Juma'a ne aka samu labarin yadda wasu 'yan bindiga suka kutsa cikin kotu, suka sheke wani alkali
  • Kungiyar NBA ta nemi gwamnati ta gaggauta daukar mataki don kiyaye faruwar hakan a nan gaba

Jihar Imo - Kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta fusata, ta bayyana bacin ranta da yadda aka kashe wani alkali lokacin da yake yanke hukunci a kotu a jihar Imo.

Kungiyar ta yi Allah-wadai da yadda ‘yan bindiga suka hallaka mai shari'a Nnaemeka Ugboma a karamar hukumar Oguta a jihar da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, BBC ta ruwaito.

Bacin ran kungiyar na fitowa ne daga cikin wata sanarwar da sakataren yada labaranta Akorede Habeeb Lawal ya fitar, inda ya tabbatar da kisan alkalin a ranar Juma’a 3 ga watan Janairun 2023.

Kara karanta wannan

Toh fa: CBN na kuntatawa talakawa da sunan hukunta 'yan rashawa, inji sanata Shehu Sani

NBA ta yi Allah-wadai da kisan alkali a Imo
Kungiyar Lauyoyi Ta Yi Martani Mai Zafi Bayan ’Yan Bindiga Sun Kashe Alkali Yana Tsaka da Yanke Hukunci | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wasu wadanda suka ga lokacin da aka yi kisan sun ce, an harbe alkalin ne bayan da ya kammala yanke wani hukunci kan wata shari’a da ke gabansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kwace wayoyin jama'a, an kashe alkali

A cewarsu, an ga isowar ‘yan bindigan ne da yawansu, kuma da zuwansu kotun suka karbi wayoyin kowa da ke ciki kana suka bindige alkalin.

Kungiyar ta ce kisan Ugboma babban abin damuwa ne, kuma kisan ma’aikatan shari’a na kokarin zama ruwan dare a Najeriya.

A bangare guda, ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar mataki tare da kare ‘yan Najeriya a duk inda suke, The Nigerian Lawyer ta ruwaito.

Hakazalika, ta nemi a tura jami’an tsaro a harabar duk wani kotu a jihar Imo don tabbatar da ba a sake cutar da wani ma’aikacin shari’a ba a yankin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kashe Alkalin Kotu Cikin Kotu Yana Tsaka da Yanke Hukunci

Ya zuwa yanzu NBA na ci gaba da bincike don gano makasan alkalin tare da tabbatar da an gurfanar dasu a gaban kuliya manta sabo.

Rahotonmu na baya ya bayyana yadda 'yan bindigan suka kutsa har cikin kotu suka hallaka wannan alkali.

Ya zuwa yanzu dai ba a gano musabbabin shiga wannan kotu ba, kana ba a gano wadanda suka yi barnar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel