Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Alkalin Kotu Cikin Kotu Yana Yanke Hukunci

Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Alkalin Kotu Cikin Kotu Yana Yanke Hukunci

  • Da rana tsaka, yan bindiga sun shiga cikin kotu sun bindige Alkali guda kuma ko daya ba'a kama ba cikinsu
  • Alkalin da aka kashe shine shugaban Alkalan kotun kostomaren dake karamar hukumarsa
  • Har yanzu hukumar yan sanda bata fadi komai game da wannan abin takaici da ya auku ba

Imo - Wasu yan bindiga sun bindige Alkali kuma shugaban kotun kostomaren Ejemekwuru, Nnaemeka Ugboma, har lahira ranar Alhamis, 3 ga Febrairu, 2023.

Wannan abu ya auku ne a karamar hukumar Oguta ta jihar Imo.

Leadership ta ruwaito wani mai idon shaida da cewa yan bindigan sun dira harabar kotun kan babura kuma suke garzaya kai tsaye cikin kotun ana tsaka da zama.

Ya ce nan take suka fito da alkalin waje kuma suka bindigeshi suka kama gabansu.

Kara karanta wannan

Kuyi Hakuri Da Wahalar Karancin Naira Kamar Yadda Kuke Hakuri Da Shan Magani Idan Baku Da Lafiya: Ministar Kudi

Mai idon shaidan wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace:

"Yan bindigan sun iso kan babura, suka shiga cikin kotun kuma suka fito da shi (Alkalin) duk da cewa ana kan zama. Suka bindige shi, suka hau baburansu kuma suka wuce yayin mu kuma muka gudu."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alkali
Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Alkalin Kotu Cikin Kotu Yana Yanke Hukunci Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

An tattaro cewa Alkalin na asalin garin Nnebukwu ne a karamar hukumar Oguta ta jihar.

Ya kammala karatun shari'ar a 1991.

Wani abokin aikin, Emperor Iwuala, a ranar Juma'a ya tabbatar da aukuwan lamarin inda yace:

"Dan'uwana, Alkali, Nnaemeka Ugboma, shugaban kotun kostomare Ejemekwuru Oguta LGA an harbeshi jiya a kotu. Gaskiya mun shiga cikin wani mumunan hali."

Shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya, shiyyar Owerri, Ugochukwu Allinor, shima ya tabbatar da kisan.

An Bada Belin Alkalai da Ma'aikatan Kotun Shari'ar Kano Da Ake Tuhuma da Sace Kudin Marayu N580m

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC Zasu Shiga Ganawar Sirri Da Buhari Kan Lamarin Naira Da Tsadar Mai

A wani labarin kuwa, Kotun majistare ta bada belin Alkalan kotun shari'a biyu, da wasu ma'aikatan kotu 17 da ake tuhuma da sace kudin marayu N580.2 million a jihar Kano.

Alkalin kotun, Mustapha Sa’ad-Datti, a hukuncin da ya yanke ranar Laraba ya baiwa Alkalan biyu da wasu mutum 12 beli kan Naira milyan daya kowanne da kuma mutum biyu-biyu da zasu tsaya musu.

Alkalin ya kara da sharadin cewa wajibi ne mutum daya cikin mai tsayawa kowannensu ya ajiye kudi N200,000 a asusun kotu yayind ana biyun kuwa ya mallaka dukiya a jihar Kano mai darajar N10 million.

Asali: Legit.ng

Online view pixel