Bidiyon Hamshakin Mai Kudin da ya Haukace, Yana Tikar Rawa a Kasuwa

Bidiyon Hamshakin Mai Kudin da ya Haukace, Yana Tikar Rawa a Kasuwa

  • Wani bidiyo mai ban tausayi da ke nuna halin da wani mutumi ya shiga wanda a baya ana ganinsa matsayin attajiri ya narkar da zukatan 'yan soshiyal midiya
  • An ga mutumin wanda ake tunanin ya samu tabin hankali yana kwasar rawa a tsakiyar kasuwa ba tare da sautin wani kida ba
  • An ruwaito yadda mutumin a lokacin da ya ke da lafiya ya taimaki mutane, amma a yau babu wanda ya zo nufesa don ceto shi daga kangin da ya ke ciki

An ga wani mutumi wanda a baya attajiri ne a wani bidiyo yana gararamba a kasuwa cikin yanayin tabin hankali.

Bidiyon mahaukaci
Bidiyon Hamshakin Mai Kudin da ya Haukace, Yana Tikar Rawa a Kasuwa. Hoto daga TikTok/@saka_hero
Asali: UGC

Wani mai amfani da yanar gizo ya wallafa bidiyo mai ban tausayi a dandalin TikTok yayin da ya labarta yadda mutumin ya aiwatar da rayuwarsa lokacin da duniya ta aure shi.

Kara karanta wannan

Bidiyo mai Narka Zuciya: Yara Marayu Suna ta Tsalle da Murna a Bidiyo, Suna Hayewa Jikin Mai Kula Dasu Bayan Ya Dawo Daga Tafiya

Kamar yadda mai amfani da kafar TikTok din ya bayyana, mutumin da ba a fadi sunansa ba ya kasance na kwarai, wanda ke taimakon mutane da dukiyarsa, amma a yau, babu wanda ya zo don kawo masa dauki.

"Wannan mutumin a da hamshakin attajiri ne, wanda ke taimakon mutane da dama amma dubi abun da ya faru da shi yau, hmmm babu wanda ya san mai gobe za ta haifar."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Kamar yadda ya rubuta.

A faifan bidiyon, an ga yadda mahaukacin ke kwasar rawa a tsakiyar kasuwa sanye da tsumman tufafinsa.

Martanin 'yan soshiyal midiya

RICH AUNTY ta ce:

"Wani ne ya sa masa hannu."

Nana Yaw ta ce:

"Wata kila kawai dai ya na farin ciki ne...Masu kudi suna yin abun ban dariya wani lokaci."

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Bidiyon Tsohon da Yayi Shekaru 61 ba Bacci Kuma Yana Raye a Duniya

user3711119968182 ya ce:

"Ka san Afirka muna da mutanen banza ina tunanin wani ne ya jefes hi da mumman abu ka san mutane basa wasa da mutanen da basa kauna."

jesuslove ya ce:

"Yawwa ka yi tunanin daga inda ya samu dukiyarsa...shedan ba zai taba bada abu ba ba tare ya tabbatar da karshenka ya wulakanta a bainar jama'a ba."

Sterphie ta ce:

"An kai shi asibitin mahaukata kuwa? Yana da tabin hankali don haka yana bukatar taimako, ba komai ka gani bane asiri."

Cindy for real ya ce:

"Hmm kawuna ya na fuskantar irin wannan yanayin, ina zubda hawaye duk lokacin da na ga yana iyayyakun nan."

FGambrah ya ce:

"Tushen dukiyarmu a Ghana abun tamabaya ne. Koda yaushe Ubangiji na taimakon mutamin don tare dukiya. Hanyar arzikin 'yan Ghana na da ayar tambaya."

Leburori sun daga abokin aikinsu cancak bayan ya ci jarabawarsa

Kara karanta wannan

Miji Nagari: 'Dan Najeriya ya ba Matarsa Kyautar Adaidaita Sahu 2 Ranar Zagayowar Haihuwarta

A wani labari na daban, wasu leburori sun daga abokin aikinsu sama kacokan yayin da suke tsaka da aikinsu.

Labarin cin jarabawarsa ne ya riske su. Sun dinga rawa sun taya shi murna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel