Bidiyo: Kacokan Leburori Suka Daga Abokin Aikinsu Bayan Samun Nasara a Jarabawarsa

Bidiyo: Kacokan Leburori Suka Daga Abokin Aikinsu Bayan Samun Nasara a Jarabawarsa

  • Wani lokaci ne cike da tsananin farin ciki yayin da wani Lebura ya samu labari mai dadi kan yadda ya ci jarabawarsa da maki mai yawan gaske
  • Yana tsaka da aiki a wani kamfanin kwangila ne yayin da labarin mai dadi ya riskesa, inda abokan aikinsa suka tayashi murna
  • A wani bidiyo da ba kasafai aka saba gani ba na taya murna, sun daga shi saman kafadunsu tare da kwasar rawa a wurin inda aka dauki faifan bidiyon da ke tashe

Wani bidiyon minti uku na TikTok ya bayyana yadda wata tawagar leburorin suke taya abokin aikinsu murna wanda ya lashe jarabawarsa.

Lebura da abokan aikinsa
Bidiyo: Kacokan Leburori Suka Daga Abokin Aikinsu Bayan Samun Nasara a Jarabawarsa. Hoto daga TikTok/@sammyskmjengo.
Asali: UGC

Yaron wanda ke aji na hudu na aiki da wani kamfanin kwangila ne yayin da labarin mai dadi game da jarabawarsa ya riskesa.

Yaron ya fara wakoki gami da kwasar rawa bayan labarin ya riskesa, inda abokan aikinsa leburori a wurin kwangilar suka taya sa murna.

Kara karanta wannan

Bidiyo:Matar aure ta Kama Mijinta Dumu-dumu da Budurwarsa a Wurin Cin Abinci, An Tafka Dirama

Cikin mintoci kadan din, laburorin sun shirya kansu gami da fara wakoki da raye-raye a wurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A matsayin wani fannin taya murna, laburorin sun daga dalibin aji 4 saman kafadunsu gami da zagawa dashi suna taka rawa.

Rawan da taya murna ya cigaba na mintoci.

Haka suka cigaba da kwasar rawa na mintoci yayin da suka dakatar da aikinsu don taya dalibin aji 4 murnar nasarar da ya yi.

Martanin 'yan soshiyal midiya

@olivwrwabwire ya ce:

"A wurina, hakan bai yi yawa ga 'A' din ba, hakan yafi ga dabi'ar! Yanzu yana kan fuskantar rayuwa ne da mayar da hankali da shekaru yayin da tsararrakinsa suke daukar kayan nauyi daga wannan wurin zuwa wani gurin a cikin rukunnan gidaje. Hakan abun farin ciki ne."

@TruphyH ya ce:

"Wannan shi ne tsantsan kauna. Tushen mu. Ina taya dalibin murna da irin nasarar da ta tunkarosa a gaba a wurin aikinsa."

Kara karanta wannan

Yadda Dalibi Ya Mayar Da Dakin Kwanansa Na Makaranta Ya Zama Karamin Kanti, Yana Ciniki Sosai

@bena_mukuria ta yi tsokaci:

"Wannan hakikanin kwarin guiwa ne daga zuciyoyin wadannan mazan."

Bidiyo mai taba zuciya, Gwamna yana addu'a kan gawar 'dan

A wani labari na daban, hoton gwamna Abdullahi Sule kan gawar 'dansa yana zuba masa addu'a ya taba zukatan jama'a.

Hassan Sule ya rasu yana da shekaru 36 bayan angwancewarsa da watanni bakwai a garin Lafia da ke jihar Nasarawa bayan fama da gajeriyar rashin lafiya da yayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel