Bidiyo Mai Narka Zuciya: Yara a Gidan Marayu Suna ta Tsalle da Murnar Dawowar Mai Kula dasu

Bidiyo Mai Narka Zuciya: Yara a Gidan Marayu Suna ta Tsalle da Murnar Dawowar Mai Kula dasu

  • Wani bidiyo da ke tashe na wasu yara masu kayatarwa suna maraba da zuwan wani mutumi gidan marayu ya jano cece-kuce a soshiyal midiya
  • A bidiyon, yaran cike da farin ciki sun rugo da gudu zuwa ga wani mutumi gami da rungumeshi cikin walwala da farin ciki
  • 'Yan soshiyal midiya sun yi martani game da abun da suka tsinkaya yayin da yawanci ke ganin mutumin na da matukar kirki

Wani mai ma al'umma hidima, wanda ke da gidan marayu ya narkar da zukatan jama'a bayan yaransa sun tarbe shi da wani salo na daban.

Gidan Marayu
Bidiyo Mai Narka Zuciya: Yara a Gidan Marayu Suna ta Tsalle da Murnar Dawowar Mai Kula dasu. Hoto daga @AbdulQahar_AQ
Asali: Twitter

Mutumin mai karancin shekaru ya yi tafiya zuwa wani wuri da ba a bayyana ba, sai dai, ya yi nisa daga yaran na wani lokaci.

Yayin da ya dawo, ya ziyarci gidan marayun, inda yaran suka yi farin cikin ganinsa. Sun garzayo gami da rungume shi, yayin da wasu suka yi tsalle garesa cike da fari nciki maras misaltuwa a fuskokinsa.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Bidiyon Tsohon da Yayi Shekaru 61 ba Bacci Kuma Yana Raye a Duniya

Abdul Qahar ne ya wallafa bidiyon a dandalin Twitter da tsokacin:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wani mai hidimtamawa al'umma, wanda shi ne mai gidan marayu bayan dawowarsa daga wata tafiya. ALLAH SHI ba mu ikon taimakon marayu. Amin."

Martanin 'yan soshiyal midiya

Ibrahim Muhammad ya ce:

"Waye wannan bawan Allan? Farin cikin da ke fuksokin yaran nan kawai zai iya kai shi Aljanna."

Suraiya ta yi tsokaci:

"Wannan kadai zai iya nuna yadda yake kyautatawa yaran, kuma suna matukar yabawa."

Umar Abdul ya yi martani:

"Tsantsar so da farin ciki. Yadda ya ke mu'amala da su subhanallah, abun da taba zuciya."

Pankoo ya ce:

"Hmm.. Wannan shi ne alamar arziki mai amfani. Ubangiji Allah ya cigaba ta cika masa burinsa. Allah ka bamu ikon taimako musamman na kasa da mu. Ameen."

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Gansamemen Saurayi Ya Shiga Tashin Hankali Yayin da Za a Masa Allura Ya Ba Da Mamaki

Jameela ta ce:

"Maganar gaskiya na zubda hawaye, musamman lokacin da yaran suka yi tsalle kan shi. Allah ya biya shi da Aljannar Firdausi. Ameen."

Arc Wasiu ya kara:

"Wannan shi ne arziki mai amfani. Mutane da dama na jefa farin ciki a fuskoki."

Soyayya gamon jini: Dirarrar budurwar ta auri wada

A wani labari na daban, wata dirarrar budurwa ta bayyana hotunanta cikin bidiyo da mijinta wada.

Ta sanar da cewa tana kaunarsa kuma sun zaune cikin farin ciki, lamarin da yasa jama'a aka dinga mata Allah sam barka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel